1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shari'ar Diezani Alison-Madueke

Uwais Abubakar Idris
April 6, 2017

Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da tsohuwar ministar mai ta kasar Diezani Allison-Madueke bisa zargi na bada cin hanci ga ma'aikatan hukumar zabe.

https://p.dw.com/p/2aoVN
Österreich Wien 166. OPEC Konferenz
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Pfarrhofer

Wannan zargi da ake wa tsohuwar ministar kula da harkokin mai ta Najeriya Nigeria Diezani Alison-Madueke a gaban kotu da ma yadda daya daga cikin ma'aikatan hukumar zabe ya amsa cewa lallai ta bashi cin hanci na Naira milyan 30 kuma ya karba babban lamari ne a tuhume-tuhume da hukumar yaki da halasta kudaden haram ta EFCC ke gabatarwa a kan wannan batu.

Nigeria Port Harcourt Arbeiter auf Plattform Ölförderung
Masana'antar man fetur ta Najeriya na daga cikin wuraren da ake zargin ma'aikata na yin rub da ciki da dukiyar kasarHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Baya ga batu na bada cin hanci ga ma'aikatan hukumar zaben Najeriya din don sauya alkaluman zabe na shakrar 2015, har wa yau kotu na zargin tsohuwar ministar da karkatar da kudi Naira biliyan 23 wanda ya kasance daya daga cikin zarge-zarge na nuna halin bera da akewa tsofaffin jami'an gwamnati.

Zargin rub da ciki kan dukiyar kasa da har yanzu ake ci gaba da bankadowa tamkar almara ya sanya masharhanta da 'yan kungiyoyi na fararen hula da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar bayyana takaicinsa bisa ga irin koma-bayan da irin wannan ta'ada ke haifarawa musamman ga kasashe masu tasowa.

Yayin da kotu ke tuhumar ita wannan tsohuwar minista da kuma irin fadi-tashin da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ke cigaba da yi na bankado masu halin bera don gurfanar da su gaban shari'a a share guda kotu ta wanke alkalin wata babbar kotu a kasar wato mai shari'a Adeniyi Ademola daga duk wani laifi bayan da aka ambato sunansa cikin wanda ake zargi da karbar na goro.