1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya da batun cinikayya a Afirka

June 27, 2019

Bayan share tsawon shekara guda ana ta jan kafa, daga dukkan alamu Tarayyar Najeriya na shirin sanya hannu kan yarjejeniyar ciniki ta kasashen Afirka bayan da wani kwamiti da gwamnatin kasar ta kafa ya ce ba haufi.

https://p.dw.com/p/3LCZX
Äthiopien AU-Gipfel in Addis Adeba
Shugabannin kasashen Afirka na son fara kasuwanci mara shinge a tsakanin kasashensuHoto: Getty Images/AFP/M. Tewelde

Duk da cewar dai tana zaman kasa mafi yawan al'umma kuma kasuwa mafi girma a nahiyar Afirka, Tarayyar Najeriyar dai ta ja baya ga bukatar rattaba hannu a yarjejeniyar kasuwancin mara shinge ta nahiyar. Babbar hujjarta dai na zaman tsoron mai da ita zuwa jujin kayayyakin waje da ma kila matattara ta shige da ficen da babu ka'ida a cikinsa.

To sai dai kuma wani kwamiti da gwamantin kasar ta kafa da nufin ba da shawarwari, ya ce ba haufi idan kasar ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar tare da tabbatar da kare muradunta. Kwamitin mai wakilai 44 da kuma ya kunshi masu ruwa da tsaki a harkokin ciniki da kasuwanci  a kasar dai, ya mika rahoto ga shugaban kasar tare da bayyana cewa yarjejeniyar ka iya tasiri ga makomar kasar.

Ya zuwa yanzu dai rashin iya kula da kan iyakokin Tarayyar Najeriyar ya mayar da ita bola ta shigar kaya na kasashen waje ta hanyoyin kasashe makwabtanta. Abun jira a gani dai na zaman yanke hukuncin karshe a kan yarjejeniyar daga Tarayyar Najeriya da ke shirin karbar bakuncinr taron kasashen Afirka nan da makwanni biyun da ke tafe.