1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sojoji sun kashe jagoran 'yan fashi a Zamfara

Salissou Boukari MNA
March 10, 2018

Jami'an tsaro a Tarayyar Najeriya sun tabbatar da kashe shugaban barayin shanun nan da ake kira "Baharin Daji" da ya addabi jihar Zamfara da ma wasu jihohi makwabta.

https://p.dw.com/p/2u4rf
Nigeria Soldaten
Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

Yayin wani taron manema labarai, shugaban hukamar tsaro ta farin kaya wato DSS da ke kula da jihar ta Zamfara Hadi Usman Sudawa, ya tabbatar da wannan batu na kashe jagoran barayin shanun na jihar ta Zamfara.

Jami'an tsaron sun kuma nuna gawar shugaban maharan ga bainar jama'a don gujewa duk wata jita-jita. A baya dai mutumin da ake kira da sunan Baharin Daji, shi ne ke jagorantar mahara wadanda ke kai hare-haren da suka yi sanadiyyar rasa rayukan jama'a da dama, da dimbin dukiyoyi.

Ko a 'yan kwanakin baya-bayan nan ma, sai da mahara suka kai wani hari a kauyukan da ke karamar hukumar Zurmi a jihar ta Zamfara inda suka kashe mutane sama 30.

A watan Disamba na shekara ta 2016 gwamnatin jihar ta Zamfara gami da jami'an tsaro suka yi wata yarjejeniya ta tsagaita buda wuta da Baharin Ddajin, inda ya yi alkawarin daina kai hare-haren amma kuma daga bisani ya saba alkawarinsa.