Najeriya za ta shiga yarjejeniyar ciniki maras shinge
July 3, 2019Talla
Kasar da ta fi karfin tattalin arziki a nahiyar ta Afirka a farko, ta nuna rashin gamsuwa kan yarjejeniyar ta African Continental Free Trade Agreement AfCFTA sai dai bayan dogon nazari da ta ce ta yi da kwararru ne ta amince, kamar yadda fadar gwamnatin ta wallafa a shafinta na twitter.
Ana sa ran shugaban zai sanya hannu a yarjejeniyar a yayin taron Kungiyar tarrayar Afirka karo na hamsin da biyar da zai gudana a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar a karashen wannan makon. Ciniki maras shinge, acewar masana tattalin arziki, zai taimaka wajen fitar da kasashen nahiyar baki daya daga kangin talauci da ma kuma samun karfin fada a ji a tsarin hada-hadar kasuwanci a duniya.