1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta yi kashedi ga 'yan jarida

Gazali Abdou Tasawa
January 8, 2019

Gwamnatin Najeriya ta gargadi kafafen yada labarai na kasar kan su yi taka-tsantsan wajen bayar da labarin kan yaki da Boko Haram domin kauce wa saka sojojin kasar a cikin hadari a daidai lokacin da suke fagen daga. 

https://p.dw.com/p/3BD9i
Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

Ministan yada labarai na kasar ta Najeriya Lai Mohammed ne ya yi wannan gargadi a lokacin wata fira da 'yan jarida inda ya ce gwamnatin najeriya ba ta da nufin tauye 'yancin aikin jarida a kasar, amma kuma ya kamata a cikin aikin nasu kafafan yada labarai su iya rarrabewa tsakanin 'yancin fadar albarkacin baki da kundin  tsarin mulkin kasar ya ba su da kuma yada labaran da ka iya zamowa barazana ga tsaron lafiyar kasar. 

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai wasu sojoji da jami'an hukumar leken asirin cikin gida ta kasar suka kai samame a cibiyar jaridar Daily Trust a birnin Maiduguri inda suka tattare kayan aikin jaridar tare ma da iza keyar ma'aikatanta, biyo bayan wani labari da jaridar ta Dely Trust ta buga a shafinta na farko kan wasu bayanan sirri na sojojin kasar da suka hada da tasawirar shirin da sojin suka yi na neman karbo birnin Baga na yankin Tabkin Chadi daga hannun mayakan Boko Haram.