1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta gargadi sojojinta da 'yan Biafra

Mohamed Bello/GATNovember 13, 2015

Hukumomin sojin Najeriyar sun yi wannan jan kunne ne a cikin wata sanarwa bisa lura da rashin kulawa da ka'idojin aikin tsaron kasa daga wasu rukunonin sojojin kasar ,

https://p.dw.com/p/1H5VX
Nigeria Symbolbild Armee Soldaten Offiziere
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Gbemiga

A sakamakon la'akkari da rashin kulawa da kaidojin aikin tsara kasa na wasu rukunonin sojojin Najeriya da a kan turasu aikin kwantar da tarzoma don kare salwantar rayuka da dukiyoyi, rundunar sojin Najeriya ta fidda wata takardar jan kunne ga daukacin sojojin kasar da a kan tura irin wadannan aiyyuka na musamman a kasar, da su guji dauka bangare a aikin nasu, kuma rundunar ta nunar za ta sa kafar wando daya da duk wadda aka kama da laifi. Haka kuma ta ja kunnen 'yan tarzomar san kafa kasar Biafra.

Gargadin hukumar sojin Najeriya ga sojojinta

Wannan sanarwa dai ga sojojin na Najeriya da hukumar rundunar Sojin kasar ta fidda a baya bayan bnan, na da nufin ankarar da sojojin kan tanade-tanaden da ke cikin ka'idojin aikin soja, musamman ta fannin aiwatar da aikin ko ta kwana, a sakamakon ballewar rikici, tashin hankali,ko mummunar zanga-zanga a ko ina a fadin Kasar.

Nigeria Armee rettet Mädchen Symbolbild
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Ikechukwu

A wannan sanarwar dai da aka nunar ta fito daga ofishin mai rikon mukamin daraktan hulda ja Jama'a na sojojin Najeriyar, ta bayyana rashin jin dadinta dangane da yadda ire-iren wadannan aiyyukan na musamman da sojin kan gudanar, inda aka samu halayyar rashin nuna kishin kasa, lamarin kuma da rundunar ta ce ba za ta sake lamunta ba. Hukumar sojin dai ta ja hankulan Sojoji da yin la'akkari da irin umarni da akan basu na su yi amfani da dukkan karfi don tunkarar aikin samar da zaman lafiya a kasa.

Sai dai wani batu da ke daukar hankali ,shi ne na umarnin da hukumar sojin ta yi na cewar za a iya bude wuta kan duk wani mutuman da Jami'an tsaro da ke a guraren bincike suka umarta da ya tsaya kuma ya ki tsayawa. kan haka nema 'yan kungiyar kare hakkokin dan adam suka fara magana.

Kungiyoyin kare hakin dan Adam na adawa da umarnin hukumar sojin Najeriya

Madam Florence ita ce jami'a a kungiya kare hakkokin bil adama ta stake Holder Democracy Network a Niger Delta Najeriya :

"Mun yadda cewar hukumar sojin Najeriya hukuma ce da ke da dokoki da ka'idojin aikin tsaro, sai dai mu kuma da zaman 'yan kare hakkoki na bil adama, ba mu yadda da a kashe mutane ba haka kawai, dole ne sai an ba su dama ta gurfana gaban sharia don fuskantar laifin da ake zargin sun aikata tukuna, saboda in har a ka yi amfani da karfi to tirjiya ce za ta biyo baya"

Rundunar sojojin Najeriyar dai tunatar da sojojin kasar na cewar babu haufi in an yi amfani da karfin soji yayin da yanayi ya tabbatar akwai bukatar hakan, musamman in wani daga cikin Jami'an tsaro ko wasu, ko kuma wadanda ake bai wa kariya sun fada mummunan yanayi, to a nan ana iya bude wuta ko da kuwa babu umarnin yin hakan daga kwamandan ko wace irin rundunar sojin tsaro, to amma fa kawai in babu isasshen lokacin jiran wannan umarni.

Soldaten im Kampf gegen Boko Haram in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa

Jami'a 'yar kare hakkoin biladama Madam Florence ta kara cewa.

"A gaskiyya bai kamata a bude wuta kan mutum ba, domin yin hakan na nufin mai bude wutar ya zama kotu ,kuma ya zama Jami'in sharia ,muna cikin yanayi na dimokradiyya da ke da tsarin dokokin kasa wadanda ya kamata abi kafin yin wata aika-aika kan ko wane mutum".

Hukumar sojin kasar dai haka kuma ta ja kunnen 'yan rajin son ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biafra,da a 'yan kwanakinnan ke tsananta gudanar da zanga-zanga a kasar, da cewar za ta sa kafar wando daya da su.

Tuni dai aka fara gabatar da wasu 'yan Kungiyar ta Biafra da aka kama yayin zanga-zangar ta baya-bayan nan, wadda munanta, wasu ke ganin ya sa rundunar ta sojin Najeriya ta yi jan kunnen da tayi.