1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta nada sabon shugaban rundunar yaki da Boko Haram

Gazali Abdou TasawaJuly 30, 2015

Janar Ilya Abbah zai jagoranci rundunar hadin guiwar kasashen yankin tafkin Chadi ta MNJTF da za ta yi yaki da kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1G7WP
Nigeria Soldaten
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Tarayyar ta Najaeriya ta nada Janar Ilya Abbah a matsayin sabon shugaban rundunar hadin guywar kasashen kewayen yankin tabkin Chadi da za ta yaki da Kungiyar Boko Haram. Janar Iliya Abbah wanda yake Musulmi ne dan asalin yankin Arewacin kasar ta Najeriya, ya kasance a baya shugaban rundunar sojojin Najeriya da ke yaki da tsagerun Niger Delta a yankin Kudancin kasar.

Janar din zai jagoranci sabuwar rundunar hadin guiwar kasashen yankin tafkin na Chadi mai suna MNJTF wacce ta hada kasashen Najeriya, Nijar, Chadi, Kamaru da kuma Benin. Rundunar za ta kunshi sojoji 8700 kuma cibiyarta za ta kasance a birnin N'Djamena na kasar Chadi.

Sabuwar rundunar za ta maye gurbin tsohuwar rundunar hadin guiwar wacce ta kunshi kasashen Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru wacce daga farkon watan Febraru na wannan shekara kawo yanzu ta yi samu galaba da dama a kan kungiyar ta Boko Haram ba tare da amma ta yi nasarar karya lagonta ba.