Najeriya ta nemi hadin gwiwar Makwabtanta
February 26, 2014Najeriya ta yi kira ga makwabtan a, kasashe renon Faransa na Afirka ta Yamma, musamman ma kasar Kamarun, da su dafa a kokarin magance matsalar Boko Haram tun kafin su fara kai ga muradu na Faransa.
Da yake magana Ministan yada labaru na kasar ta Najeriya Labaran Maku, ya ce "ni a ganina, ya kyautu mu hada karfi da karshe da faransawa, da kasashen dake anfani da harshen faransanci na Afirka ta yamma, muddin dai ana so a magance wannan matsala."
Wannan kira ya zo ne 'yan sa'o'i kadan kafin ziyarar da shugaban kasar Faransa François Hollande, zai kai a kasar ta Tarayyar Najeria a wannan Alhamis (27.02.14), wanda zai kasance babban bako mai alfarma a bukin zagayowar hadewar kasar a matsayin dunkulallar kasa.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohammed Abubakar