1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta sami sabon Sufeto-Janar

August 1, 2014

Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da nadin Suleiman Abba a matsayin sabon babban Sufeton 'yan sandan Najeriya abin da yazo daidai lokacin da kasar take cikin mummunan hali a fannin tsaro.

https://p.dw.com/p/1CnWb
Suleiman Abba, Generalinspektor der nigerianischen Polizei
Suleiman Abba, sabon Sufeto-Janar na yan sandan NajeriyaHoto: DW/U. Musa

A ci gaba da yunkurinta na neman mafita ga batun rashin tsaron da ke kara ta'azzara a sassa daban daban na arewacin kasar ta Najeriya, gwamnatin kasar ta kai ga nadin sabon babban Sufeotn yan sandan da zai dauki alhakin tabbatar da tsaro dama kila kaiwa ga zabukan dake tafe.

Wata sanarwar fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock ce dai ta kai ga tabbatar da nadin na Suleiman Abba da ke zaman daya a cikin mukaddasan manyan Sufetocin yan sandan kasar da kuma ke da jan aikin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a sassa daban daban na kasar.

Nadin na Suleiman da yazo a dai dai lokacin da batun rashin tsaron a sashen arewacin kasar yake kara yake kara ta'azara dai na iya bude sabon babi ga kokarin kaiwa ga ganin bayan annobar Boko Haram din dake nuna alamar zama da gindin ta cikin kasar a halin yanzu. Abba da ya rike mukamai daban daban cikin gidan yan sandan ne dai a karkashin kundin tsarin mulkin kasar ke da babban alhakin tabbatar da komai daidai ga Tarrayar Najeriyar, da sunan ta ke zaman ta kan gaba ga batun ta'addanci a duniya baki daya, mutumin kuma da daga dukkan alamu ya samu karbuwa har ga adawar kasar da ke fadin suna fatan sauyin in har masu mulkin kasar suna shirin barinsa tabbatar da aikin sa a kan hanya a fadar Buba Galadima da ke zaman jigo a adawar da kuma yace yai nisa a sanin babban jagoran yan sandan.

“ Ina tabbatarawa al'umma cewar nasan Suleiman Abba farin sani, don tare da shi mukayi aiki a gwamnatin Abacha. Mutum ne mai saukin ka,i mai tausayi, saboda duk zarge-zargen da ake yiwa jami'an tsaron da sukai aiki da Abacha ban ga mutum daya da ya nuna yatsa kan Suleiman Abba ba. Da naji labarin nada shi na yi masa murna, na kuma yi masa kuka saboda sanin gwamnatin ba zata taba kyale yayi aikinsa kamar yadda ya kamata ba”.

Aiki a tsakaninsa da Allah ko kuma kokari na tsomin baki a cikin aikin dai, babban kalubalen dake gaban sabon babban Sufeton yan sandan na zaman tunkarar matsalar rashin tsaron dake kara ta'azzara cikin kasar, da ma kila kaiwa ga zabukan tarraya a cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a farkon shekarar dake tafe. Kalubalen kuma da a cewar Garba Umar Kari, dake zaman wani masani ga zamantakewa ke zaman jan aiki ga shugaban yan sanda a cikin yanayin da sojan kasar suka tabbatar da kwace aikin yan sandan amma kuma suka gaza tabbatar da biyan bukata ta yan kasa.

“A sanin kowa ne cewar dama tun tuni ita wannan matsala ta Boko Haram ta fita hannun yan sanda, soja sun yi dumu-dumu, mai yiwa saboda kazancewar harkar, mai yiwuwa kuma saboda halin ko-in-kula da aka nunawa yan sanda. To saboda haka in aka yi tsamanni Suleiman Abba zai iya wani abu kan harkar Boko Haram to ba ayi masa adalci ba, saboda sojoji ke wannan fada su din ma kuma kwalliya bata biya kudin sabulu ba”

Polizeiposten in Millionenstadt Kano, Nordnigeria
Nauyin tsaro a wuyan yan sandaHoto: Katrin Gänsler

Abun jira a gani dai na zaman takun nasa a tsakanin al'ummar kasar da ma gwamnatin dake fadin tana shirin ganin karshen matsalar Boko Haram a cikin wasu watanni hudun dake tafe.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu