1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta sanar da ranara jigilar alhazai

Usman ShehuAugust 22, 2013

Hukumar kula da aikin hajji, ta sanar da ranar 14 ga wata Satumba a matsayin ranar fara jigilar maniyyata zuwa hajji.

https://p.dw.com/p/19Uru
epa02992433 Muslim pilgrims perform Friday prayer around the holy Kaaba in the center of the Haram Sharif Great Mosque, on the first day of the Muslim's Haj 2011 pilgrimage, in Mecca, Saudi Arabia, 04 November 2011. According to the Muslims holly book the Quran, the Kaaba was built by Abraham and his son Ismael, after Ismael had settled in Arabia. Millions of Muslims arrived in Saudi Arabia to perform their Hajj. The Hajj 2011 is due to take place from 04 to 09 November. EPA/AMEL PAIN
Dakin Ka'abaHoto: picture-alliance/dpa

Gwamantin Najeriyar ta sanar da matakan aikin Hajjin bana saboda kaucewa abinda ya faru a bara. Yanzu dai a ranar 14 ga watan Satumba mai zuwa aka ajiye a matsayin ranar da za'a fara jigilar mahajjatan kasar zuwa Saudiyya.

Sanar da ranar da za'a fara jigilar mahajattan Najeriyar zuwa kasar ta Saudiyya dai, muhimmin mataki ne a shirye-shiryen da aka dade ana yi domin gagarumi kuma muhimmin aikin jigilar mahajattan kasar da a duk shekara ke zama aiki da ke ciki da kalubale.

GetyImages 131611057 Muslim pilgrims throw pebbles at pillars during the 'Jamarat' ritual, the stoning of Satan, in Mina near the holy city of Mecca, on November 6, 2011. Pilgrims pelted pillars symbolising the devil with pebbles to show their defiance on the third day of the hajj as Muslims worldwide marked the Eid al-Adha holy day with mass animal sacrifices. AFP PHOTO/FAYEZ NURELDINE (Photo credit should read FAYEZ NURELDINE/AFP/Getty Images)
Mahajjata wajen jifan shaidanHoto: AFP/Getty Images

Sanin irin matslalolin da Najeriyar ta fuskanta a shekarar da ta gabata inda rashin muharami ga mata mahajatta ya haifar da matsalolin, da ya sanya maido da wasu da dama a bana hukumar tace dole ne ko wace mace ta kasance da muharamminta. To sai dai duk da fara shiri da wuri akan fuskanci matsaloli na jinkiri da ma zargin kamfanonin da aka baiwa aikin gaza kulawa da bukatun mahajattan, ba tare da ganin zahirin hukuncin da aka yi masu. Malam Muhammad Musa Bello shugaban hukumar aikin hajjin Najeriyar yace a bana kam ba sani ba sabo.

"Abinda muka shaida masu shine dole ne kowa ya tsaya ya yi aiki tsakaninsa da Allah, an san wannan harka ce ta kasuwanci, amma kada su manta cewa duk fasinjan da suke dauka za su je kasar Sa'udiyya ne, domin wata ibada da ke da muhimmanci a addinin Islama. Don haka su tabbatar da sun cika alkawarin da suka yi wa kowane Alhaji, kuma duk kamfanin da ya saba alkawari to za'a hukunta shi. Abinda ya faru bara ya riga ya faru, kuma ba zai sake faruwa ba domin an dauki matakai a kan hakan''

Wer hat das Bild gemacht?:Aminu Abdullahi Wann wurde das Bild gemacht?:26.09.12 Wo wurde das Bild aufgenommen?:Saudi Arabien Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Pilgerinnen aus Nigeria in Saudi Arabien
Mniyyatan najeriya da suka samu matsala a SaudiHoto: DW

A yayinda kalilan daga cikin mahajattan Najeriyar da suka samu nasarar shiga cikin jerin wadanda ke sa ran sauke farali a wanan shekarar, mahajatta da dama suna ci gaba da nuna damuwa a kan yadda ake tafiyar da aikin, musamman jigilar da akan baiwa kamfanonin jiragen sama. Alhaji Abubakar Ibrahim ya dade yana aikin hajji a Najeriya, kuma ya bayyana irin abubuwan da suka fuskanta.

"Maganar aikin hajji a Najeriya kullum za ka ji shugabanni su ce an gyara an gyara, amma maganar dai tana nan guda ce, za'a yi kokarin jigilar mahajatta a kan lokaci, amma wajen dawowa sai a yi ta sa maku rana, amma sai a kai sati biyu ba'a kwasheku ba, karshe lokacin da za'a zo a daukeka alhaji ya kashe kudinsa, abinci ma a wahalce yake samunsu.''

Wanan ya sanya na tauntubi Alhaji Ibrahim Dahiru jami'in yada labaru na Max Air, wanda shine kamfanin da ya fi jigilar mahajattan masu yawa daga Najeriya, don jin me zai ce bisa ga korafin da aka dade ana yi game da kamfanonin jigilar alhazan Najeriyar.

Sultan Sa'ad Abubakar III. Stichworte: Nigeria, Sultan, Sa'ad Abubakar III., Sokoto Sa'ad Abubakar III. ist seit 2006 Sultan von Sokoto und damit spirituelles Oberhaupt der Muslime in Nigeria. Offizielles Foto, copyright: Sultan's Office
Sarkin musulman Najeriya Sa'ad Abubakar III.Hoto: Sultan's Office

"Akwai shirye- shirye da yawa da muka yi ko yaushe mukan kalli matsalolin da muka fuskanta a kowace shekara, zamu zauna mu dubi wadanan matsaloli domin a gyara su, dama matsalolin na rashin isassun jirage ne, kuma a wannan karon muna da su. Insha Allahu za mu yi aikin nan cikin sauki tare da yardara, mu koma ranar da aka kammala, za mu iya dawo da mahajattan nan''

A bana dai mahajattana dubu 76 suka samu nasarar shiga cikin jerin wadanda ke fatan sauke faralli a kasar ta Saudiyya, maimakon dubu 99 da akan tura, saboda zabtare kashi 20 cikin dari na mahajattan da mahukutan kasar Saudiyya suka yi ga kowace kasa. A bin jira da ma fata shine, ganin fara aikin jigilara da za'a fara daga ranar 14 ga watan Satumba mai zuwa.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris

Edita: Usman Shehu Usman