1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dole a ciwo bashi don kasafin kudin 2021

June 25, 2021

Shugaban majalisar dattijan Najeriya sanata Ahmed Lawal yace babu gudu babu ja da baya sai an ciwo bashi don aiwatar da kasafin kudi na shekarar 2021

https://p.dw.com/p/3vZLz
Nigeria National Assembly
Hoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Akalla dalar Amurka miliyan dubu biyar ne dai mahukuntan tarrayar Najeriya suka ce suna da bukata da nufin iya aiwatar da kasafin kudin kasar na shekarar bana. Kasafin kuma da aka yi shi cikin halin babu, amma kuma tarrayar Najeriyar ke kallon karuwar kudin shiga sakamakon tashin farashin man fetur.

To sai dai daga dukkan alamu majalisar dattawan kasar tace dole ne cin bashin kafin mahukuntan kasar su iya aiwatar da manya da kananan aiyyukan da 'yan kasar ke bukata.

Shugaban majalisar dattawan sanata Ahmed Lawal dai yace duk da karuwar farashin man Najeriya bata da kudin gina layin dogo da sake farfado da manyan hanyoyi balle batun wutar lantarki da ingantar harkar noma. Lawal din dai yace gwamnatin kasar ta talauce, kuma babu batun kara haraji da 'yan kasar ke ta korafi.

Ya zuwa yanzu dai yawan bashin dake kan kasar ya kai Naira triliyan 33 adadin da tuni ya fara jawo fargaba a ciki da wajen Najeriyar. 'Yan kasar dai na da tunanin bashin na neman mayar da hannun agogo baya na sake fadawa cikin kuncin bashi. Kusan daya a cikin uku na yawan kudin kasar dai ya zuwa yanzu na tafiya ne wajen biyan kudin ruwa na dumbin bashin da kasar ta ciwo a baya.

To sai dai a fadar shugaban majalisar dattijan ba hali a tsaida manyan aiyyukan kasa da aka fara saboda rashin kudi da Najeriyar ke fama da shi a halin yanzu.

A fadar Yusha'u Aliyu dake zaman masanin tattalin arziki akwai hanyoyi da dama na tara kudade ba tare da an koma cin bashi ba.

Abujar dai na tsakar ruwa a kokarin sake ginin sabbabin hanyoyin layin dogo da manyan tituna, ko bayan shirin inganta wutar lantarki da gwamnatin ke kallo na iya tasiri ga bunkasa tattalin arzikin da ya dauki lokaci yana tangal-tangal.