1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta tsaurara tsaro a iyakarta da makwabta

August 23, 2019

'Yan kasuwa a Najeriya, na kokawa kan wani matakin da suke zargin mahukunta ne suka dauka dangane da rufe iyakar kasar da wasu kasashe makwabta, abin kuma da ke shafar harkokinsu na kasuwanci.

https://p.dw.com/p/3OOsi
Lagos Port Hafen Nigeria
Hoto: AFP/Getty Images

Ita dai wannan iyakar ta kasance kafa ce ta kasuwanci a tsakanin kasashen yammacin Afirka, inda Najeriya ke zama abar koyi saboda karfinta na tattalin arziki da ya sanya hada-hadar hajoji daga ketare ta yawaita saboda yawan al’umma da kuma bukatu. Sai dai samun  bayanan sirri ya sanya kwatsam daukar matakin rufe iyakar duk da kasuwancin da ke a tsakani, koda yake wasu majiyoyi na gwamnati sun karyata batun rufe iyakokin.

Bayanai daga iyakar Seme Border da ke iyaka da kasar Benin, na nuni da cewa a yanzu manyan motocin dakon kwaya da na zirga-zirgar jama’a na girke a iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin, koda yake masu kananan harkoki na kasuwanci na gudanar da ‘yan hada-hadar da ba a rasa ba.

Sai dai a daya hannun akwai jita-jitar cewa wasu tireloli masu dakon kaya musamman masu samun alfarma, amma wasu ‚‘yan kasuwa na karyata batun. Manya da kananan ‘yan kasuwa dai sun zuba ido don ganin yadda za a wanye a wannan lamarin da gwamnati ta ce ta yi shi a bisa dalilai na tsaro.