1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lalube cikin duhu kan tsaro a Najeriya

May 6, 2021

A ci gaba da kokarin neman mafitar rikicin rashin tsaron da ke dada rikidewa a cikinTarayyar Najeriya, majalisar dattawan kasar ta share tsawon wuni guda tana ganawa da manyan hafsoshin tsaro da rundunonin sirrin kasar.

https://p.dw.com/p/3t4Wj
Nigeria | Präsident Muhammadu Buharitrifft neue Militär Chefs in Abuja
Sababbin afsoshin tsaron Najeriya tare da Shugaba Muhammadu Buhari a tsakiyarsuHoto: Ubale Musa/DW

Sun dai share tsawon kusan sa'o'i biyar suna ganawar sirri. Daya bayan daya kuma 'yan majalisar dattawan kasar suka rika yi wa sababbin manyan hafsoshin tsaro na Najeriyar tambayar ya aka yi, a cikin rikicin rashin tsaron da ke nema ya wuce da sani na kasar. Ganawar da ke zaman irinta ta farko a tsakanin dattawan da sabbabin jami'an tsaron dai, na zaman wani sabon yunkuri na hadin gwiwa a tsakanin bangarorin dokoki da na zartarwa da nufin tunkarar matsalar da ke barazana ga makomar kasar.

Karin Bayani: Martani kan zargin yin juyin mulki a Najeriya

Dama dai hafsoshin sun share tsawon kwanaki biyu suna ganawa da shugaban kasa, a wani abun da ke zaman zube ban kwarya bisa harkar ta tsaro. Kuma a fadar Sanata Ali Ndume da ke zaman shugaban kwamitin kula da aikin soja a majalisar dattawan, ganawar na zaman mai tasirin da babu kamar ta a lokaci mai nisa. Majiyoyin zauren taron dai sun ce ra'ayi yazo iri guda, na bukatar sake bai wa manyan hafsoshin daukacin bukatu na kudi da sababbin kayan aiki na zamani da nufin tunkarar jerin matsalolin da kalubalen tsaron da suka rikide ya zuwa bakar siyasa a kasar.

Nigeria Politik l Senat
Majalisar dattawan Najeriya na kokarin shawo kan matsalar tsaro a kasarHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Mustapha Salihu dai na zaman jigo a cikin jam'iyyar APC mai mulki da kuma ya ce lokaci yana nema ya kure wa daukacin kasar da ke neman siyasa da batun tsaron da ke zaman mai hatsari a Najeriyar. Koma ya zuwa yaushe ake shirin zuwa cikin nema na hadin kai na 'yan kasar dai, daga dukkan alamu ana shirin ganin farin hada kan tun daga zauren majalisar.

Karin Bayani: Zargin yankurin juyin mulki a Najeriya

A cewar Sanata Ndumen 'yan majalisar sun amince su bayar da hadin kai ga 'yan uwansu na bangaren zartarwa domin fitar da kasar daga cikin matsalar rashin tsaron. 'Yan mulkin na Abuja dai na fuskantar kari na matsin lamba daga masu adawa na kasar da ke fadin tsintsiyar ta gaza share dattin rashin tsaron da ta alkawarta daga farko.