1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Boko Haram ya karu a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 28, 2018

Shugaban Najeriya Mhammadu Buhari ya bukaci sojojin Najeriya da su kara kaimi wajen yakar 'yan ta'addan Boko Haram da suka addabi Najeriyar da makwabtanta.

https://p.dw.com/p/395Mf
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari bei Militär in Maiduguri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ziyarasa a MaiduguriHoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Muhammadu Buhari ya yi kira ga sojojin ne yayin wata ziyara da ya kai birnin Maiduguri a wannan Larabar, kwana guda gabanin tafiyarsa zuwa N'Djamena babban birnin kasar Chadi domin halartar wani taro na gaggawa tsakanin shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da Chadin, da nufin lalubo hanyar kakkabe mayakan na Boko Haram. Yayin da yake yin jawabi ga tawagarasa a taron sojoji a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno da ke zaman babbar cibiyar 'yan Boko Haram din, Buhari ya yabawa sojojin Najeriyar da ya ce sun yi kokari matuka wajen rage kaifin kungiyar tun lokacin da ya hau karagar mulki a shekara ta 2015 kawo yanzu. 

Boko Haram na ci gaba da kisa

Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Sababbin hare-hare a kan sojoji da fararen hula daga Boko Haram a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Duk da bugun kirjin da gwamnati ke yi na cewa ta ci karfin kungiyar ta Boko Haram dai, kungiyar na kai hare-hare a kan sojoji da fararen hula. Ko da a ranar 18 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki ma dai, kungiyar ta kai hari kan sansanin sojoji a kauyen Metele tare da hallaka sojoji 43, koda yake wasu sojojin da suka tsira da ransu, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa yawan sojojin da kungiyar ta hallakaya kai 100. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP AFP din ya ruwaito cewa akawai rahoton yunkurin kai hari a kan sansanin sojoji cikin watan Yulin da ya gabata har sau 17, daga kungiyar ISWAP da ke zaman wani bangare na Boko Haram da ya balle.