1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisa sun karbi takardun samun nasara

Uwais Abubakar Idris MNA
March 14, 2019

A yayin da 'yan majalisar dokokin Najeriya suka karbi takardun samun nasara domin shirin majalisa na fara aiki nan gaba, manyan 'yan majalisar da dama sun fadi a zabe. Yaya tasirin wannan a siyasar Najeriyar?

https://p.dw.com/p/3F3Hx
Ginin majalisun dokokin Najeriya da ke Abuja
Ginin majalisun dokokin Najeriya da ke AbujaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

'Yan majalisar dattawan da suka karbi takardun nasu na samun nasara daga hukumar zabe na cike da murna da farin ciki, a zauren taro na kasa da kasa a Abuja. Akwai dai tsaffi da kuma sabin kamu a jerin 'an majlisar inda jamiyyar APC mai mulki ke da rinjaye na 'yam majalisa 63 ita kuma PDP ta 'yan adawa na da 37, jam'iyyar YPP na da guda daya. Sanata Ahmed Lawan na cikin tsaffin 'yan majalisar da sau shida ke nan ana fafatawa da shi.

"Za a rika samun zaman doya da manja tsakanin wakilan jam'iyyu dabam-dabam musamman APC da PDP domin manufofin jam'iyyun ba daya ba ne. Fatanmu shi ne a samu hadin kai tsakanin APC mai rinjaye da PDP da ke zama shugabar marasa rinjaye."

Akwai sabbin 'yan majalisa da suka samu shiga a yanayin da aikin majalisar ke cike da kalubale mai yawan gaske. Sanata Uba Sani daga jihar Kaduna na mai bayyana cewa.

"Za mu shiga majalisa don kare muradun talakawa mene ne bukatun al'ummarmu amma ba don ra'ayin kanmu ba."

Bukola Saraki shi ne shugaban majalisar dattawa da ya fadi a zabe
Bukola Saraki shi ne shugaban majalisar dattawa da ya fadi a zabeHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Irin yadda jiga-jigan 'yan majalisar suka sha kashi a zabe na gaza komawa majalisa kama daga shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Sanata Godswill Akpabio ya zuwa George Akume, baya ga gwamnonin da suka yi yunkurin shiga majalisar irin su Rochas Okorocha da Abiola Ajimobi na samar da sabon babi a siyasar Najeriyar, inda mutanen da suke jin sun kafa daula, a yau daular ta fara wargajewa. Shin wannan na nuna fara kawo karshen siyasar uban gida ne a Najeriyar? Dr Usman Mohammed masanin kimiyyar siyasa ne da shi ne shugaban kungiyar kula da ayyukan 'yan majalisu a Abuja.

"A hannun daya wannan na nuna cewa dimukuradiyya na bunkasa, kuma ana zaban wanda ake so ya je majalisa. To amma kuma a wani hannun yana nuna ci-baya ga ayyukan majalisa, domin za su koma koyon aikin majalisa tsawon shekaru kafin su samu gogewa."

An dai ga raguwar matan da suka samu shiga majalisar abin da ke nuna koma baya.

Tuni dai aka fara sabuwar siyasa ta neman shugabancin majalisar dattawan.