1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan siyasa na dagula tsaron Najeriya

May 15, 2019

Janar Tukur Buratai ya yi wannan zargi yayin da yake jawabi ga mambobin kwamitin kula da harkokin sojoji na majalisar wakilai ta Najeriya.

https://p.dw.com/p/3IZAi
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari bei Militär in Maiduguri
Shugaba Buhari da Janar Yusuf Buratai a tsakiya a wani zama kan harkokin tsaroHoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Babban hafsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya zargi 'yan siyasa da suka fadi zabe da hannu wajen karuwar hare-haren 'yan bindiga da sace mutane a yi garkuwa da su don neman kudin fansa wanda ake fama da shi a shiyoyin Arewa maso Yammaci da Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

"Kalubalen tsaro da muke fuskanta yanzu haka, ina da yakini na cewa ba za a rasa alakanta shi da zaben da aka kammala ba da dadewa ba, wasu 'yan siyasa da suka fadi zabe na daukar nauyin aiyukan na bata gari muna da shedu masu karfi, sai dai muna taka-tsantsan don kauce wa kuskure." 

Janar Buratai ya yi wannan zargi yayin da yake jawabi ga mambobin kwamitin kula da harkokin sojoji na majalisar wakilai ta Najeriya wadanda suka je Maiduguri fadar jihar Borno domin samun bayanai a kan yadda ake samun tabarbarewar tsaro a Najeriya.