1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yawaitar cin hanci tsakanin ma'aikata

Uwais Abubakar Idris SB
August 17, 2017

Rahoto da hukumar kididdigar jama’a tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya suka fitar ya ce Naira milyan dubu 400 ne ma’aikatan gwamnati suka karba a matsayin cin hanci a shekara daya a Najeriya.

https://p.dw.com/p/2iQ2C
Nigeria Symbolbild Korruption
Akalla Naira milyan dubu 400 ne ma'aikatan gwamnati suka karba a matsayin cin hanci cikin shekara daya a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Wannan adadi  na Naira bilyan 400 da ma'aikatan gwamnatin Najeriyar ke karbewa a matsayin cin hanci a cikin shekara guda kacal, ya nuna cewa kashi 32.3 cikin 100 na ‘yan kasar da suka mallaki hankalinsu ya zame masu tillas ne su ba da abin da ake kira na goro, yayin da wasu kuma ake tunkararsu domin su ba da cin hancin.

Nuna ‘yar yatsa a kan ma'aikatan gwamnatin Najeriyar a kan batun cin hanci da rashawa dai muhimmi ne, musamman yadda rahoton da ke da sa hannun hukumar gwamnati ya nuna cewa bangaran ‘yan sandan Najeriyar, da kuma fannin shari'a ne suka fi kowa karbar cin hanci bayan kuwa su ne ake wa kallon madafa ta karshe wajen kare talaka daga wannan matsala.

Nigeria Plakate und Aufkleber gegen Korruption
Karuwar cin hanci a tsakanin ma'aikatan gwamnati a NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

A daidai lokacin da wannan ke faruwa sai gashi wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, abin da ke jefa tsoron illar da hakan zai yi ga yakar masu halin bera. Tuni dai kungiyoyin fararan hula suka mayar da martani tare da yin Allah wadai ga harin da aka kai.

Akwai fatan cewa a wannan karon rahoton zai yi tasiri ta fanin daukan mataki daga gwamnati, ganin cewar tana da masaniya a wannan rahoton da ya nuna ‘yar yatsa ga lamarin cin hanci da rashawa a kasar, wanda ke haifar da koma baya ta kowane bangare.