1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zabe don kawo karshen rusau

March 6, 2019

Badia na daya daga cikin unguwannin talakawa a birnin Legas a Najeriya. Akasarin mazauna wannan unguwa dai na rayuwa ne cikin tsofaffin rumfuna, inda da wuya ka ga mai gidan sauro, balle dakunan bahaya da na wanka.

https://p.dw.com/p/3EXSl
Nigeria Lagos - Wahlkampf: Wählerkarten
Hoto: DW/K. Gänsler

Wannan unguwa ta Badia da ke kan babban titin da ya raba tashar jiragen ruwa ta Apapa da filin jiragen sama na birnin na Legas da ke zama cibiyar kasuwancin Najeriyar dai, ana iya ganin tantunan da mutane ke rayuwa ciki a gefen layin dogon da tuni aka daina amafani da su.

Deji Akinpelu ya mayar da wannan unguwa tamkar matsuguninshi na biyu. Fitaccen mai daukar hoto kuma dan fafutuka na yawaita ziyartar wannan unguwa yana daukar hotuna. 

Nigeria Lagos - Wahlkampf: Fotograf Deji Akinpelu
Deji Akinpelu mai daukar hoto da fafutukaHoto: DW/K. Gänsler

Idan Deji ya ziyarci unguwar, ya kan dauki hotunan irin yadda suke rayuwa yana sakawa a dandalin sada zumunta na Facebook, domin wasu su samu damar ganin yadda rayuwar wasu ke wakana, musamman 'yan siyasa. Wasu lokuta ya kan zanta da 'yan unguwar, kuma hirarsu akan abubuwa biyu ne: Zaben gwamnoni a ranar Asabar da kuma rusau da rabasu da muhallinsu da aka yi a watan Disambar 2018. 

Abiye Oluwatoyin Shodele na daya daga cikin mazauna wannan unguwa ta Badia, wadda ta kasa mance abun da ya rutsa da su a wannan rana ta 12 ga watan Disambar shekarar da ta gabata. Ta ce ba tare da wata sanarwa ba, kawai sai suka ji jami’an gwamnati sun afka masu, bayan fesa hayaki mai sa hawaye suka harbe ta.

Tun daga shekarata ta 2013, unguwannin talakawan na Legas ke fuskantar rusau, wanda ke tilasta fitar da mutane daga matsugunensu ba tare da samar musu wasu ba. Kashi biyu daga cikin ukun al'ummar Legas miliyan 22 talakawa ne, hakan ke nufin su ne masu taka rawa a zabukan gwamna da na 'yan majalisar jiha, sai dai bisa dukkan alamu ba sa cikin lissafin 'yan takara 45 din.

Nigeria Lagos - Wahlkampf: Armut,
Rayuwa a gefen tsohon layin dogoHoto: DW/K. Gänsler

Mai daukar hoto Deji Akinpelu na kokarin ganin cewar an fitar da dan takarar kujerar gwamna daga irin wadannan unguwanni na talakawa da ke legas, domin su ne za su iya sanin halin da mazauna irin wadannan unguwanni suke, musamman na rashin matsugunai da tarin juji da makamantansu. Emmanuel Oladele Ojuri shi ne mai magana da yawun mazauna unguwar ta Badia, ya ce gwamnati ta siyar da yankinsu ga masu kudi duk kudinsa na fansho sun kare a gina gidan da yake ciki amma an kwace.

Babatunde Gbadamosi ganau ne na yadda cikin gajeren lokaci unguwa ta zame tarin kasa cikin watan Janairu. Zai tsaya takarar gwamna a karkashin tutar jam'iyyar ADP da aka kafa a shekara ta 2017. Ya dauki lokaci yana ganawa da 'yan unguwar ta Badia, da kwadaita musu sauyin rayuwa idan ya yi nasara. Hausawa dai sun ce rana ba ta karya.