1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ja'maa na ci gaba da fitowa

Abdourahamane Hassane
February 23, 2019

Duk da fashewar wasu abubuwan da aka samu a Maiduguri da ke a yankin arewa maso gabashin Najeriya da sahin safiyar yau yanzu haka wakilinmu na yankin ya shaida cewar zaben na ci gaba da gudana lami lafiya.

https://p.dw.com/p/3DxRd
A nan wata mazabar ce a Jihar Zamfara inda jama'a ke jefa kuri'a
A nan wata mazabar ce a Jihar Zamfara inda jama'a ke jefa kuri'aHoto: DW/Yusuf Ibrahim

'Yan bindiga sun kai hari a Maiduguri da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya sa'o'i kalilan kafin bude runfunan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu, lamarin da ya tilasta wa mutane gudu gabanin fara kada kuri'a. To sai dai a halin yanzu al'amura sun daidaita kuma jama'a na ci gaba da halartar runfunan zabe domin ka'da kuri'unsu.