1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya:Takun saka tsakanin gwamnati da Avengers

Muhammad Bello/AHJune 10, 2016

Ƙungiyar tsagerun na Niger Delta ta ce ba ta san da tattaunawar neman sulhu ba tsakaninta da gwamnatin Tarrayar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1J4c1
Karikatur Gespräche mit Militanten im Niger-Delta?
Hoto: DW

Bayanai na cewar zaman tattaunawar sulhu da wakilan gwamnatin Najeriya suke nuni da cewar yana gudana, Avengers ta musunta furcin kana kuma tana ci gaba da kafewa cewar ba ta san da batun wannan zama ba.

Ƙoƙarin shawo kan 'yan bindigar na Niger Delta domin shiga tattaunawar

Har jiya da dare,wakilan gwamnatin Tarraya da suka haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan shirin Afuwar 'yan bindigar na Niger Delta Brig Gen Paul Boro sun yi ta ƙoƙarin shawo kan Avengers ɗin da su amince a tattauna amma kuma ba tare da cimma nasara ba.

Nigerdelta Angriff Rebellen
Hoto: picture alliance/dpa

Ci gaba da kai hare-hare a kan manyan kamfanonin mai na Yankin Niger Delta

'Yan Bindigar na Yankin na Niger Delta,shi ne na ci gaba da kai hare-hare ko a daren jiya sai da suka tarwatsa wani layin bututun na kamfanin NNPC da ke surkukin ruwayen Shalomi a ƙaramar hukumar Warri ta kudu a Jihar Delta.

Nigeria - Brennende Ölpipeline
Hoto: picture alliance/dpa/dpaweb

Abin da ya haddasa rage addadin ƙarfin wutar lantarkin ƙasar da MW 1500,sannan kuma da safiyar yau sun tarwatsa wani bututun na mai mallakar kamfanin Agip .dama kuma shekaran jiya sun kai wa bututayen man kamfanonin mai na Chevron da Shell hari,inda yanzu kimanin Naira biliyan kusan 20 Najeriya ke asara a sakamakon wannan tsaiko.