1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nasarar rigakafin cutar Ebola

Usman ShehuNovember 27, 2014

Kwarraru a kasar Amirka sun tabbatar da nasarar gwajin rigakafin cutar Ebola kan mutane, lamarin da ya bada haske kan shawo annobar da ke halaka mutane

https://p.dw.com/p/1DuNc
Genf Einlieferung Felix Baez Sarria Ebola Patient 21.11.2014
Hoto: AP Photo/Julien Gregorio, Geneva University Hospital

Masu bincike kan samamar da rigakafin cutar Ebola a Amirka, sun bayyana matukar gamsuwarsu bisa sakamakon da suka samu. A karon farko gwajin da aka yi kan wasu mutane ya nuna alamar maganin zai bada kariya daga kamuwa da cutar. Kamar dai yadda aka gani a gwajin da aka yi kan dabbobi, gwajin farko kan mutane ma ya nuna za a iya samun kariya daga maganin cutar Ebola. A yanzu haka dai hukumar kula da magungunan Amirka bisa hadin gwiwa da wasu kamfanonin hada magani suna aiki ba kama hannun yaro, bisa lalubo maganin cutar Ebola, da ma samar da riga kafin kamuwa da ita. Kawo wannan lokacin alkaluman wadanda cutar ta hallaka ya kai sama da mutane dubu biyar, akasarinsu a yammacin Afrika.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu