1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO za ta taimaki Tukiya da makaman kariya

December 5, 2012

Ƙungiyar ƙawance tsaro ta NATO ta ta yi na'ame da buƙatar ƙasar Turkiya na girke mata makaman kariya daga makamai masu lizami

https://p.dw.com/p/16w1l
NATO-Russland-Rat Brüssel Anders Fogh Rasmussen NATO Secretary General Anders Fogh Rasmussen speaks at a media conference during a meeting of NATO foreign ministers at NATO headquarters in Brussels on Tuesday, Dec. 4, 2012. NATO foreign ministers are expected to approve Turkey's request for Patriot anti-missile systems to bolster its defense against possible strikes from neighboring Syria. (Foto:Yves Logghe/AP/dapd)
Hoto: AP

Tun a cikin watan jiya ne ƙasar ta Turkiya ta gabatar da wannan buƙata ga ƙungiyar tsaron ta NATO domin samun makaman da ta ke son a gigirke mata akan iyakar da ta raba da Siriya har ta kilomita 900, dangane da barazanar da ta ke fuskanta ta harbin makaman iguwa daga Siriyar.Wanda a makon jiya wasu makaman iguwan da Siriyan ta harba suka faɗa a cikin ƙasar ta Turkiya abin da ya kiɗimar da shugabanin waɗanda ke ganin a kwai buƙatar samun samfarin makaman da zasu iya cafke makaman masu luzami da aka ya harbo wa.

Ya zama wajibi NATO ta bai wa Turkiya Makaman kariya saboda Siriya

Sannan sanarwa da wani babban jam'in ƙasar Amurka ya baiyana a farkon wannan mako cewar Siriya na shirin hada makamai masu guba shi kansa ya zama abinda taron na bruxelle ya tattauna.Da yake yin magana a wanan taron babban sakataran ƙungiyar ƙawancen tsaron ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya ce NATO za ta kare Turkiya.Ya ce'' mun sanni Siriya ta na da makamai masu lizami waɗanda ke cin dogon zango da kuma makamai masu guba yan ce dole ne a cikin lisafin mu na taimaka wa Turkiya kuma ya ce idan Siriya ta kuskura ta yi amfanin da makamai masu guba to zata gamu da fushin ƙasashen duniya.

ARCHIV: Eine Luftabwehrrakete vom Typ "Patriot" wird zu Testzwecken abgeschossen (Foto undatiert). Die Bundeswehr wird offenbar in Kuerze Flugabwehrraketen mit deutscher Bedienungsmannschaft an die tuerkisch-syrische Grenze verlegen. Nach Informationen der "Sueddeutschen Zeitung" (Samstagausgabe vom 17.11.12) will die Tuerkei am Montag (19.11.12) eine offizielle Bitte an die NATO richten, zum Schutz ihres Territoriums Raketensysteme des Typs Patriot zur Verfuegung zu stellen. Der NATO-Oberkommandierende in Europa, James Stavridis, wolle dieser Bitte umgehend entsprechen. Die Bundeswehr werde sich mit einer oder zwei Patriot-Staffeln und bis zu 170 Soldaten an der NATO-Operation beteiligen. Ob dazu ein Mandat des Bundestags erforderlich ist, pruefe die Bundesregierung derzeit. (zu dapd-Text)
Makaman KariyaHoto: dapd

Zargin da ake yi wa Siriya na amfani da makamai masu guba akan alummarta

Amurka da Jamus da Hollanda zasu ba da gudun moya ta wasu naurorin haɗa makaman masu lizami da zaran majalisun dokokin ƙasashen sun amince da shirin abin da ake gani watakila shi zai sa a samu jinkiri wajan isar da makaman ga Turkiya.Amma allah kuli hali ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce dole ne su yi wanan agaji.Ya ce'' bayar da wannan gudumo wa ya zama haki ga ƙawance ƙasahen ƙungiyar ya ce idan kuma aka hana to a kwai mumunar sakamako ga ƙasashen ƙungiyar.

Syrian President Bachar Assad, center, arrives at the Elysee Palace prior to a meeting with French President Nicolas Sarkozy in Paris, Saturday, July 12, 2008. (AP Photo/Jacques Brinon)
Bachar Al Assad shugaban SiriyaHoto: AP

Ƙasashen Siriya da Rasha da kuma Iran na addawa da shirin ƙungiyar NATO

Siriya dai ta musunta zance da ta ce zargi ne kwai na yin amfani da makamai masu guba akan al 'ummarta yayin da kuma kasashen Rasha da Iran suka yi kakausar suka ga shawara kasashen ƙungiyar tsaron .Minstan harkokin wajan Rasha Serge Lavrov wanda ya halarci taro na Brussel ya gargadi ƙasashen duniyar da ka'da suka aikata kuskure akan jita jitar cewar Siriyar na da makaman guba wanda ya ce su kan su ba su amince dasu b. To amma ministan harkokin waje na ƙasar Holand ya ce ba shi ne matsalar ba .Ya ce ''ina tsamanin a matsyin mu na menba na ƙungiyar tsaro ta NATO ya zama nauyi akan mu na kiyaye tsaro akan iyakokin mu koda ma wannan magana bata taso ba, ya ce sam wannan lamari ma baya da alaƙa da abin da ke faruwa a Sriya kwai dai zamu ɗauki matakan kare Turkiya.Za a iya kwashe makonnin dai nan gaba kafin Turkiya ta samu waɗanan makamai ,sai dai kafin nan masu yin sharhi akan al'amura na yin tsokacin cewar ya kammata ƙasashen duniyar su yi taka tsan tsan akan shelar da aka yi cewar ƙasar Siriya zata yi amfani da makamai masu guba;domin kada a sake yin irin kuskuren da aka yi akan Iraki cewar gwamnatin margagni Sadam ta mallaki makaman ƙare dangi.

Russian President Vladimir Putin (R) speaks with newly appointed armed forces Chief-of-Staff Valery Gerasimov (L) and Defence Minister Sergei Shoigu during their meeting in Moscow's Kremlin November 9, 2012. REUTERS/Alexsey Druginyn/RIA Novosti/Pool (RUSSIA - Tags: MILITARY POLITICS) THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Vladimir Putin shugaban Rasha a fadarsaHoto: Reuters

Mawallafi:Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Awal

Daga ƙasa za a iyasauraron wannan rahoto