1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nau'in Ebolar Kwango ba ta da karfin ta yammacin Afirka

August 27, 2014

Bullar Ebola a Kwango ta kara wa jama'a fargaba tunda an gano cewa tana da nau'o'i daban-daban kuma kowanne na da irin na sa dafin wanda idan ba a gani da wuri ba, zai yi lahani sosai.

https://p.dw.com/p/1D2d8
Symbolbild Ebola Labor
Hoto: picture-alliance/dpa

Tun bayan da ta tabbata cewa cutar Ebola ce ta bulla a yankin nan mai surkukin dajin da ke arewa maso yammacin Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango, hukumomin kiwon lafiyar kasar suka dukufa wajen yada labarai na fadakarwa ga al'ummar wannan kasa, musamman ma ta yankin gabashin kasar, da su kauracewa duk wata ma'amala da dabbobin daji, kamar su Jemage, wanda ke daya daga cikin namun dajin da al'umomin wannan kasa ke ci.

Ana iya cewa wannan dai shi ne karo na bakwai da wannan kasa ta Kwango ke fuskantar annobar cutar Ebola, wadda kuma da ma cuta ce da ta fara bulla a wannan yanki na Equateur da ke surkukin dajin arewa maso yammacin wannan kasa, a shekarar 1976 inda masanan kimiyya na kasar Beljiyam suka gano wannan kwayar cuta, sai gashi kuma wannan cuta ta sake bulla a wannan yanki da ta fara bulla yau da shekaru 38 da suka gabata.

Kwayar cutar da ke Kwango ta bambanta da ta yammacin Afirka

Sai dai kuma masana kimiyya sun sanar cewa wannan kwayar cutar ta Ebola ta kasar ta Kwango, ta sha bamban da wadda ake fuskanta a halin yanzu a kasashen yammacin Afirka. Kamar yadda daya daga cikin manyan likitoci na babban ofishin kula da bincike kan cututuka irin su Ebola mai cibiya a birnin Anvers na kasar Beljiyam, ya shaidawa DW.

"Lallai ba za a gama wannan kwayar cuta ta Ebola ta nan Kwango da wadda take wakana a kasashen Afirka ta yamma ba, domin ita waccan ta fi saurin kisa sabanin wannan da ke da kashi 20 cikin 100 wanda ya kamu da cutar ya ke da kan hadarin ya mutu, yayin da waccan akasarin duk wadanda suka kamu da ita na mutuwa ne. Kuma ana iya cewa kasar Kwango cibiya ce ta cutar Ebola dan haka babu mamaki dan yanzu an samu bullar wannan cuta a wannan kasa."

Ebola-Aufklärung in Liberia
Taron fadakarwa kan EbolaHoto: John Moore/Getty Images

Likitoci kamar su Josias Kathungu a wannan kasa ta Kwango, sun dukufa ne wajen ganin cewa al'umma ta daina cin wannan nama na Jemage da ma wasu sauran namun daji musamman ma a yankin gabashin kasar ta Kwango inda ma ba a kai ga fara samun bullar cutar ba inda yake cewa..

"Dabbobi matattu ko ma masu rai, akasari su ne cibiyar wannan cuta ta Ebola, to ta kasance muna ma'amala da su a daidai lokacin da ake fama da annobar wannan cuta, to fa akwai hadarin a samu yaduwar cutar, dan haka ya dace a yi hattara."

Kusan mutane 1500 ne suka rasu sakamakon cutar ta Ebola a kasashen Liberiya, Saliyo, Guinea da kuma Najeriya wadda ta kasance annobar cuta mafi muni da aka gani a halin yanzu tun daga bullar sa a watan Maris na wannan shekara ta 2014.

Mawallafa: Peter Hille/Salissou Boukari
Edita: Pinado Abdu Waba