1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nazari game da sabon rikicin da ya barke a Iraki

January 7, 2014

Masana harkokin yankin Gabas ta Tsakiya sun gargadi fira ministan Iraki Nuri al-Maliki da ya sauya manufofinsa dangane da mabiya darikar Sunni domin dakile rikicin.

https://p.dw.com/p/1Amhj
Irak Gewalt Ramadi Falluja Islamisten Militanten Al Qaida Al Kaida
Hoto: Reuters

A yayin da dakarun gwamnatin Iraki ke ci gaba da fafutukar kwato wasu yankunan kasar da suka fada karkashin ikon 'yan tawayen kungiyar ISIL da ke neman yin aiki da shari'ar Musulunci a wasu yankunan kasar, wadanda kuma ke samun goyon bayan kungiyar al-Qa'ida, masana harkokin yankin Gabas ta Tsakiya sun bayyana cewar, bisa la'akari da zabukan kasar da ke tafe, fira ministan kasar Nuri al-Maliki, ba shi da wani zabin da ya rage masa illa daukar matakan sauya manufofinsa, domin samun goyon bayan mabiya darikar Sunni - a fafutukar sake maido da birnin Fallujah da ya fada hannun 'yan tawayen zuwa karkashin ikon gwamnati.

A cewar Günter Meyer, masanin harkokin kasashen Larabawa da ke jami'ar Mainz anan Jamus, hada hannu da hanjaye a tsakanin gwamnatin Iraq da shugabannin mabiya darikar sunni, game da fadakarwa da kuma samun tallafi daga Amirka ne kawai ke zama hanyar magance rikicin baya bayannan da ya sanya hukumomin na Iraki rasa karfin ikonsu a wasu yankunan kasar:

Günter Meyer, Leiter des Zentrums für Forschung zur arabischen Welt an der Johannes-Gutenberg-Universität Mainz
Günter Meyer, masanin yankin Gabas ta Tsakiya, da ke jami'ar Mainz a JamusHoto: Privat

Ya ce " Muhimmin matakin cimma nasara shi ne sauyin manufa daga fira minista Nuri al-Maliki dangane da shugabannin mabiya darikar Sunni, kamar yadda ya yi musu alkawari a yanzu. Domin idan har jama'a suka fahimci manufar kuma suka bi, to, kuwa zai yi wa mayakan al-Qa'ida matukar wahala su sami gindin zama a Iraki."

Hadin gwiwa domin tinkarar rikicin Iraki

Tuni dai Amirka ta bakin kakakin fadar shugaban kasar, wato Jay Carney, ta kawar da yiwuwar tallafawa gwamnatin Iraki ta hanyar tura dakaru wajen kokarin dakile 'yan tawayen da ke yakarta a Ramadi, wadanda kuma suka kwace iko da Fallujah :

Ya ce "Sai dai kuma hakan ba ya nufin ba za mu taimaka ba, domin muna yin hakan. Muna yin aiki kafada da kafada domin mayar da kungiyoyin da ke da ala'ka da al-Qa'ida saniyar ware, kuma mun ga nasarar hakan a yankin Ramadi, inda mayakan kabilu da 'yan sanda suka hada gwiwa da sojojin Iraki, lamarin da kuma - a zahiri - ya taimaka wajen mayar da kungiyar 'yan tawayen ISIL saniyar ware a wasu yankunan birnin."

Obama trifft irakischen Ministerpräsidenten Nuri al-Maliki
Fira ministan Iraki, Nuri al-MalikiHoto: picture-alliance/dpa/dpaweb

Dalilan goyon bayan 'yan tawayen iraki

Ko da shike kungiyar 'yan tawayen ISIL da ke da'awar 'yantar da wasu yankunan Iraki da na Siriya domin aiwatar da shari'ar Musulunci ba su da goyon baya sosai a idanun 'yan Iraki saboda irin tsauraran matakan da suka dauka a yankunan da suka fada hannunsu, amma a cewar, Jochen Hippler, masanin yankin Gabas ta Tsakiya da ke cibiyar nazarin ci gaba da kuma wanzar da zaman lafiya a jami'ar Duisburg na Essen da ke nan Jamus, akwai wasu nasarorin da 'yan tawayen suka samu a baya, wadanda suka sanya al'umma yi musu kara:

Ya ce Kungiyar 'yan tawayen ISIL ta yi nasara ta fannin agazawa al'umma da abinci da kuma sha'anin kula da lafiya, inda suka yi wa sauran kungiyoyin mayakan sa kai fintinkau. Sai dai kuma tsauraran matakan da take dauka a yankunan da ta mamaye, abu ne da ke da tada hankali da kuma kuntatawa jama'a."

A yanzu ana ci gaba da fafatawa da mayakan kungiyar 'yan tawayen ISIL da kuma dakarun gwamnatin Iraki, yayin da kungiyar ke fafutukar shiga birnin Ramadi, hedikwatar lardin Anbar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani