1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman a soke zaɓe a wasu mazaɓun Kamaru

October 8, 2013

Wasu jam'iyyun siyasar ƙasar Kamaru sun shigar da ƙararraki gaban kotun koli inda suka nemi ta soke zaɓen 'yan majalisa a wasu mazaɓu saboda wasu kura-kuran da aka tafka.

https://p.dw.com/p/19wOi
Hoto: DW

Wasu jami'iyyun siyasa na ƙasar Kamaru sun shigar ƙararraki kusan 50 a gaban kotun koli don neman ta soke zaɓen 'yan majaliasar dokoki a wasu mazaɓu saboda kura- kuran da aka tafka. Jam'iyyun dai sun haɗa da RDPC mai mulki wacce ta nemi a soke zaɓen na gari Kumba da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar, inda ta zargi jami'yyar adawa ta SDF ta tilasta wa masu zaɓe kada wa 'yan takararsu ƙuri'a.

Su kuwa jam'iyyun adawa ciki har da UNDP da SDF da kuma MRC sun zargi ɓangaren da ke riƙe da madafun iko da sayen ƙuri'un jama'a musamman a mazaɓar Douala cibiyar kasuwancin ƙasar da kuma Logone da ke arewacin kamaru.Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar ta nunar da cewa an yi amfani da kuɗi a wannan zaɓe. Sai dai a nasu ɓangaren masu sa ido na ƙungiyar Tarayyar Afrika sun ce zaɓen ya gudana ba tare da maguɗi ba.Ranar 17 ga wannan wata na Nuwamba ne za a bayyana cikakken sakamakon zaɓen na 'yan majalisa. Yayin da tuni aka riga a ka samu sakamakon zaɓen a ƙananan hukumomi 360 da kamaru ta kunsa.

Mawallafi: Youssoufou Abdoulaye
Edita: Abdourahmane Hassane