1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Sauye-sauyen rabon filaye a Afirka ta Kudu

Schwikowski Martina ATB
October 16, 2018

Shekaru 24 bayan kawo karshen wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, sauyin rabon gonaki bai taka kara ya karya ba, gwamnatin tana nazarin gyara ga dokoki, wasu masana na ganin an yi watsi da wasu muhimman batutuwa.

https://p.dw.com/p/36crH
Südafrika Mankosi
Hoto: Nyani Quarmyne

Manufar ita ce domin raba filayen noma ga talakawa don magance rashin daidaito a tsakanin al'umma shekaru 24 bayan kawo karshen wariyar launin fata. Sai dai matakin na shan suka.

Sarki Goodwill Zwelithini basaraken gargajiya na kabilar Zulu ya yi kira ga shugaban kasar, yana mai rokonsa kada ya taba masa gonaki. Sarkin dai na da gona mai fadin hecta miliyan uku a gundumar KwaZulu-Natal.

eco@africa Rehabilitierung von Land in Südafrika
Hoto: DW

A hukumance dai sarakuna dai basu da wani karfi a Afirka ta kudu, sai dai suna da kima a idanun miliyoyin jama'a. Sauran sarakuna su ma sun bukaci ANC kada ta nemi ta ce za ta tozarta su.

Sai dai a cewar shugaba Ramaphosa dukkan gonar da ta dade ba a amfani da ita za a karbe a rabawa talakawa. Batun karbe filayen da sake rarraba su ga jama'a ya kasance batu mai sarkakakiya a Afirka ta kudu musamman bayan da shugaban kasar ya yi alkawarin gyaran kundin tsarin mulki domin bada halascin karbe filaye ba tare da biyan diyya ba.


Sarakuna dai kamar Zwelithini suna ganin danka gonakinsu da basa amfani da su ga manoma turawa ka iya zama wata kafa ta kaucewa kwace gonakin daga hannunsu.


Wasu dai na ganin batun gyaran kundin tsrain mulkin siyasa ce kawai domin fiye da shekaru 20 da suka wuce babu wani abu da gwamnati ta yi. Suna wannan ne kawai domin kawar da hankali daga rashin tabuka komai da basu yi ba.

eco@africa Rehabilitierung von Land in Südafrika
Hoto: DW


A shekarar 2019 da ke tafe ne dai za a gudanar da zaben yan majalisun dokoki a Afirka ta kudu. Da wannan alkawarin na gyaran dokar mallakar kasa, shugaba Ramaphosa zai fuskanci kalzbale daga jagoran adawa na jam'iyyar gwagwarmayar yancin tattalin arziki Julius Malema wanda ke bukatar daukar mataki mai tsauri na karbe gonakin manoma farar fata ba tare da biyyan diyya ba.

Ko da gyaran kundin tsarin mulkin zai zama wajibi, sai an sami amincewa tsakanin jami'yyar ANC da kuma EFF ta Julius Malema da rinjayen kashi biyu cikin kashi uku na 'yan majalisar dokoki. Sai dai kuma cimma a tsakanin bangarorin biyu na da kamar wuya.