1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafita ga matsalolin Tafkin Chadi

Salissou Boukari LMJ
April 23, 2019

Kungiyar da ke kula da raya yankin tafkin Chadi na tattaunawa a Jamhuriyar Nijar domin sanar da wasu sababbin dabaru da kungiyar ta fito da su da za su taimaka a samar da kwanciyar hankali a yankin.

https://p.dw.com/p/3HIby
Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Al'ummomi da dama rashin tsaro ya shafa a Tafkin ChadiHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Kungiyar da ke kula da raya yankin na Tafkin Chadi tare a tallafin kungiyar Tarayyar Afirka AU dai na wani rangadine, inda take tattaunawa da fannoni daban-daban na hukumomin Jamhuriyar ta Nijar domin samo mafita wadda ba ta karfin soja ba da za ta tabbatar da taro a yankin baki daya. Dabarun dai na da bangarori guda tara da suka hadar da inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya da yaki da tsattsauran ra'ayi da matsalolin canjin yanayi da kuma shimfida kyakkyawan mulki. Kungiyar ta ce ta gano yaki da ta'addanci ba zai yi nasara ba sai an yaki talauci da sauran matsaloli da ke kwadaita wa mutane shiga cikin muguwar akida.

Babban burin dai na wannan randagi da hukumar kula da raya Tafkin Chadin ke yi, shi ne na samun tabbacin cewa hukumomin kasashen na koli suna da cikakken bayani kan wadannan sababbin dubaru, ta yadda za su saukaka shimfidasu domin samun mafita. Domin cimma wannan buri dai ana bukatar cikakkiyar hulda ta hadin gwiwa tsakanin sojojin kasashen yankin kuma kungiyoyin fararen hula ma za su taka rawar gani cikin wannan tsari musamman ma a fannin fadakarwa wajen don rage tsattsauran ra'ayi daga al'umma wanda shi ne ke haddasa samun tashe-tashen hankula. Wannan tsari dai na sababbin dubarun samar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin na Tafkin Chadi, zai ci tsabar kudi miliyan dubu 12 na dalar Amirka.