1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron warware rikicin Gabas ta Tsakiya

Suleiman Babayo
January 15, 2017

Ana zaman taron warware rikicin yankin Gabas ta Tsakiya a birnin Paris na kasra Faransa kwanaki kafin kafa sabuwar gwamnatin Amirka.

https://p.dw.com/p/2Vq53
Paris Nahost Konferenz
Hoto: Getty Images/AFP/B. Guay

Jami'an diplomasiya daga kasashe fiye da 70 na duniya sun hallara a birnin Paris na kasar Faransa, domin lalubo hanoyin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Palesdinawa da Yahudawa. Yayin bude taron Shugaba Francois Hollande na Faransa ya yi gargadi kan hadrin da ke cikin watsi da shirin samar da zaman lafiya taksanin sassan biyu.

Sai dai yayin da Palesdinawa suka yi maraba da shirin, tuni gwamnatin Isra'ila karkashin Benjamin Netanyahu ta yi watsi da matakin wanda ta ce akwai lauje cikin nadi. Haka na zuwa yayin da ranar Jumma'a mai zuwa sabon Shugaban Amirka Donald Trump zai dauki madafun iko, wanda kuma ya ce neman hanyoyin sasanta bangarorin na cikin abubuwan da zai saka a gaba. Sai dai akwai shakku kan shirin sabuwar gwamnatin ta Amirka, saboda irin kalaman da suke fitowa daga bakin Trump tun kafin ya dare karagar mulki.