1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nemen tantance amfani da guba a Syriya

August 24, 2013

Majalisar Dinkin Duniya na neman shugaban Syriya ya bayar da kai ga buktaar da ta mika masa na gudanar da bincike kan zargin amfani da makamai masu guba a kan fararen hula.

https://p.dw.com/p/19Vcp
People, affected by what activists say is nerve gas, are treated at a hospital in the Duma neighbourhood of Damascus August 21, 2013. Syrian activists accused President Bashar al-Assad's forces of launching a nerve gas attack on rebel-held districts near Damascus on Wednesday that they said killed more than 200 people. There was no immediate comment from Syrian authorities, who have denied using chemical weapons during the country's two-year conflict, and have accused rebels of using them, which the rebels deny. REUTERS/Bassam Khabieh (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CONFLICT)
SHoto: Reuters

Guda daga cikin manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya Angela Kane ta isa birnin Damuscus na Siriya a wannan Asabar domin ci-gaba da yin matsin lamba ga mahukuntan Siriya kan gwamnatin kasar ta bari a kwararru su bincika zargin da 'yan adawar kasar ke yi na cewar gwamnatin al-Assad ta yi amfani da wasu makamai masu guba a 'yan kwanakin da suka gabata.

Kane ta ce jami'anta a shirye suke da su gudanar da cikakken bincike na gaskiya domin tantance tsaki da tsaba kan wannan zargi da ake na amfani da makamai masu guba wanda yanzu haka ya hallaka mutane da dama ciki har da kananan yara.

A daura da wannan, sakataren tsaro na Amurka Chuck Hagel ya ce ma'aikatar tsaro ta Pentagon na cikin shirin ko ta kwana, Ya Allah ko Amirkan ka iya yanke shawarar shiga Siriyan da yaki. Sai da shugaba Barak Obama ya ce zai yi aiki da Majalisar Dinkin Duniya wajen ganin an warware wannan matsala cikin ruwan sanyi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal