1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nepal: Girgizar kasa ta kashe mutane sama da 3000

Ahmed SalisuApril 27, 2015

Rahotannin daga kasar Nepal na cewar adadin wanda suka rasu sakamakon girgizar kasar da ta afkawa kasar ranar Asabar din da ta gataba ya haura 3000.

https://p.dw.com/p/1FFJ3
Nepal Schweres Nachbeben nach Erdbeben in Kathmamdu
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Shrestha

Mukaddashin sufeto janar na rundunar 'yan sanda kasar Komal Singh Bam ya ce bisa alkaluman da suka samu yanzu haka mutane dubu uku da dari biyu da sha takwas ne suka rasu a Nepal din baya ga 60 a kasar Indiya da kuma wasu 20 a yankin Tibet.

Masu aikin ceto suka ce dubban mutane musamman ma wanda ke yankunan karkara na cikin mawuyacin hali saboda gaza kaiwa garesu don basu agaji sakamakon lalacewar hanyoyi.

Kasashen duniya da suka hada Amirka na ta kokari wajen kai kayan agaji da nufin tallafawa wanda wannan Ibtila'i na girgizar kasa mai karfi maki 7.8 a ma'aunin Richter ya shafa kasar ta Nepal da wasu kasashen da ke makota da ita ko da dai ta'adin ya fi yawa a Nepal din.