1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: "Akwai yiwuwar Woodke na hannun MUJAO"

Gazali Abdou Tasawa
October 17, 2016

Mahukuntan Nijar sun sanar da cewa akwai yiwuwar dan Amirkan nan Jeffery Woodke wanda aka sace ranar Jumma'ar da ta gabata a Abalak na kasar Mali a hannun Kungiyar Mujao. 

https://p.dw.com/p/2RIK6
Mujao Islamisten Rebellen Mali
Hoto: Ollo Hien/AFP/Getty Images

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun sanar da cewa akwai yiwuwar dan Amirka nan Jeffery Woodke wanda aka sace a yammacin kasar a ranar Jumma'ar da ta gabata yana a halin yanzu a kasar Mali a hannun Kungiyar MUJAO mai ikrarin jihadi a yankin yammacin Afirka. 

Ministan cikin gida na kasar ta Nijar Mohamed Bazoum ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa lokacin da sojojin Nijar suka shiga farautar mutanen da suka sace Ba'amariken sun ketara da shi zuwa yankin Menaka na Gabashin kasar yankin da dama ke a hannun kungiyar ta MUJAO.

 A ranar Jumma'a da ta gabata ne dai wasu mutane dauke da makamai suka kai hari da makami a gidan Ba 'amariken  da ke a birnin Abalak na jihar Tahoua da ke a Arewacin kasar ta Nijar inda bayan sun kashe masu gadinsa suka sace Jaffery Woodke din wanda ke aiki da wata kungiyar agaji tun a shekara ta 1992 a kasar ta Nijar inda ya zamo tamkar dan kasa har yana magana a cikin yarukan kasar da dama.