1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An sace wani dan kasar Amirka a Jihar Tahoua

Salissou Boukari
October 15, 2016

Wasu mutane dauke da makammai da ba a tantance ko suwanene ba, sun sace wani ma'aikacin agaji dan kasar Amirka a garin Abalak cikin jihar Tahoua.

https://p.dw.com/p/2RGQf
Niger Soldaten in Bosso
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wata majiya ta jami'an tsaro ta shaida wa kanfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, yayin sace wannan jami'in agaji, maharan mutun biyu da suka zo kan babur, sun kashe jami'an tsaro biyu da ke bai wa jami'in agajin dan kasar Amirka kariya da wajejen karfe tara na dare na ranar Juma'a a cikin gidansa da ke cikin garin Abalak.

Majiyar ta ce, tuni dai jami'an taso daga ko ina suka ja daga tare da toshe dukannin hanyoyi masu shiga kasar Mali. Wannan dai shi ne karo na farko da aka sace wani dan kasar Amirka a kasar ta Nijar. 

Wani mai magana da yawun ofishin harkokin wajen Amirka ya tabbatar da wannan labari sai dai bai yi wani karin bayani a kai ba. A ranar bakoye ga wannan wata na Octaba ma dai wasu mutane dauke da makammai sun hallaka sojojin Nijar 22 a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Tesalit cikin karamar hukumar Tasara a jihar ta Tahoua.