1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An tsare 'yan kungiyoyin fararan hula

Salissou Boukari
November 4, 2017

Wasu jagororin kungiyoyin fararan hulla guda uku da suka gurfana a ranar Juma'a a gaban wata kotun birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar an tisa keyar su zuwa gidan kaso na garin Kollo.

https://p.dw.com/p/2n0oR
Niger Demonstration für Bildungsreform
Hoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

Mutanen uku da suka hada da Abass Abdoul-Aziz da Abdoulaye Harouna da kuma Djibo Issa na hadin gwiwar kungiyoyin kare hakin jama'a na ACTICE Niger da suka jagoranci wani taron gangami da ya gudana a birnin Yamai a ranar Lahadi 29 ga watan Octoba an tisa keyarsu ne zuwa gidan kaso na garin Kollo da ke a nisan km kimanin 20 a kudancin birnin Yamai.

Kafin dai a kama shi a ranar Litinin 30 ga watan Octoba shugaban kungiyar ta ACTICE da ke fafutikar kare hakin jama'a Abass Abdoul-Aziz ya ce ba shi da wani nauyi kan tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar nuna adawa da daftarin dokar kasafin kudin kasar ta 2018 inda ya zargi hukumomin birnin na Yamai da kin daukar matakai na bada kariya ga zanga-zangar wadda ta yi sanadiyyar jikkata 'yan sanda 23 da farfasa motoci 14 cikin su 10 na 'yan sanda kamar yadda ministan cikin gidan kasar ta Nijar Mohamed Bazoum ya sanar.