1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An tsawaita dokar ta baci a Diffa

Yusuf Bala July 30, 2016

Mahukunta a Nijar sun tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa da ke fama da kalubale na tsaro. Gwamnati dai ta ce mataki zai sanya a kara yawaita dakarun tsaro a wannan yanki.

https://p.dw.com/p/1JZ2W
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: picture alliance / dpa

Gwamnati a Jamhuriyar Nijar ta bayyana karin watanni uku a dokar ta baci da aka sanya a yankin Diffa mai fama da rikice-rikice na Boko Haram. Hare-haren mayakan na Boko Haram dai tun daga watan Mayu sun sanya garuruwan Bosso da Yebi da ke kan iyaka da Najeriya a yankin tafkin Chadi al'umma sun musu kaura, inda ya zuwa yanzu mutane dubu 69 ne suka kaurace wa muhallansu a wannan yanki kamar yadda sashin kula da agaji na al'umma a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a wani rahoto da ya fitar a ranar Juma'a. Yanzu dai wannan dokar tabaci a yankin na Diffa za ta kai har ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa, tsawaita dokar da aka rika samun kari a kanta tun daga watan Fabrairu na shekarar bara.