1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Ana cigaba da tsokaci kan yunkurin juyin mulki

Mahaman Kanta/ASDecember 18, 2015

Kungiyoyi da sauran jama'a Nijar na cigaba da tofa albarkacin bakunansu kan yunkurin juyin mulkin da aka ce wasu hafsoshin sojan kasar sun yi yunkurin yi.

https://p.dw.com/p/1HQFV
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Kungiyoyin fararen hula na Nijar dai na daga cikin wanda ke kan gaba wajen tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu inda da damarsu ke cewar yunkurin abin Allah wadai ne. Habila Rabi'u da ke jagorantar wata kungiya da ke kare hakkin matasa ya ce ''wannan lamari kokari na maida hannun agogo baya kuma ya kamata 'yan Nijar su tashi tsaye wajen kare kasar''.

Soldaten im Niger
Hukumomi sun ce wasu sojoji hudu ne suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba IssoufouHoto: Desmazes/AFP/Getty Images

Shi kuwa Masa'udu Ibrahim da ke yin fashin baki kan lamuran yau da kullum a Nijar din ya ce wannan rudani da aka shiga bai zo masa da mamaki ba duba da yadda fagen siyasar kasar a halin yanzu ya ke dumama gabannin zaben shugaban kasar da za a yi a wata mai Fabrairu da ke tafe.

To yayin da wannan batu ke cigaba da dauakr hankali a Jamhuriyar ta Nijar, shi kuwa shugaban jaam'iyyar nan ta MBDN Kokari wadda ba ta cikin jerin jam'iyyun da ke kawance da masu mulki ya ce su abinda suke son ganin an yi shi ne a yi cikakken bayani game da su wanda ake ce sun yi yunkurin juyin mulkin musamman ma sunayensu maimakon a ce ana rara-gefe.

A jawabinsa da ya yi ranar Alhamis din da ta gabata dai, shugaba Mouhamadou Issoufou ya tabbatar da wannan yunkurin na juyin mulki kuma ma ya nuna 'yar yatsa ga jam'iyyun da ke hamayya da shi kan lamari ko da dai 'yan adawar sun musanta wannan zargi nasa har ma suka kira taron manema labarai don fayyace matsayinsu.

Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Juyin mulki na zuwa gabannin zabe wanda hammayya ta yi zafi tsakanin Shugaba Issoufou da Hama AmadouHoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images