Nijar: Dalibai sun shiga yajin kaurace wa karatu

Rikici tsakanin gwamnati da dalibai na kara kamari inda daukacin daliban makarantu suka kaurace wa karatu bisa cika shekaru 7 da kisan wani dalibi a yankin Zinder da suka ce gwamnati ta kasa gudanar da bincike.

A ka'idance a wannan Alhamis wa'adin kwanaki uku da hadin gwiwar kungiyoyin dalibai da ke karatu a jami'ar Yamai ta Abdou Moumouni, da na jami'ar Zinder ke cika bisa wasu matakai na bayyana wasu jerin bukatunsu ga gwamnatin kasar da suka gindaya suna masu bukatar biyansu a cikin dan takaitaccen lokaci.

Sai dai duk da cikar wa'adin bai wuce wasu 'yan awowi kalilan da suka rage ba, hukumomin kasar ta Jamhuriyar Nijar ba su kai ga cimma wani daidaito da hadin gwiwar kungoiyoyin daliban ba, to amma sun ce sun bude wani babi na tattaunawa.

Malam Amadou Arifa shi ne babban sakataren kungiyar daliban jami'ar Abdou Moumouni da ke birnin Yamai ne da ake kira UENUN.

"Abin da muke jira da gwamnati wannan sabon salon a kawo gyaran fuska ga karatu, dole ne a sake duba shi tare da janye shi kuma muna jiran dalibai da suka yi shekaru biyu ba a biya kudaden alawus dinsu ba a biya su, saboda yau shekaru biyu ba a biya ba, kana kuma akwai wasu tarin kudaden alawus."

Rahotanni masu dangantaka

Harabar jami'ar birnin Yamai

Sai dai ko baya ga cikar wa'adin daliban jami'o'in na Yamai da Zinder, daukacin daliban makarantun bokon kasar a wannan Alhamis sun shiga cikin wani yajin aiki na wuni daya bisa dalilan rashin gudanar da wani kwakkwaran bincike game da kisan wani dalibin guda a yankin Zinder mai suna Laminou Mai Kanti wanda a wannan Alhamis yake cika shekaru bakwai da rasuwa sakamakon wata zanga-zangar da ta hada daliban kasar da jami'an tsaro.

A cewar babban sakataren kungiyar dalibai ta USN Iddar Mohamed Algabit abin na a matsayin babban abin takaici.

"Kasan gwamnatin nan ta koma maishan jini kuma shi ne na farko na dalibin da suka sha jininshi a farkon mulki, kuma yana cikin wadanda suke da dama da aka sha jininsu. To amma kuma mun lura da cewar har yau ba a yi wani bincike ba. Kenan wannan yaron da yake cika shekaru bakwai da rasuwa sun sanya shi a cikin jerin takardun mantuwa a maida abin kamar ba a yi ba."

Ministan ilimi mai zurfi Yahouza Sadissou Madobi

Bisa duk wadannan dalilan ne dai ya sanya a fusace wasu daliban Jami'ar Yamai suka tare ayarin motar ministan ilimi mai zurfi Yahouza Sadissou Madobi tare da farfasa gilashin motarsa da sacce masa tayoyi tare da kuma yin garkuwa da shi har na tsawon wani dan lokaci kan daga bisani su sallami ministan. Babban sakataren kungiyar dalibai ta kasa ya kira lamarin da cewar ya kamata ya kasancewa gwamanti darasi.

"Saboda wannan alawus din dalibai suna iya yin kashin kai. Na bara ba a ba su ba, na bana ma ba a bayar ba, kenan daliban nan cikin fushi suke matuka."

Duk kokarin da aka na don jin ta bakin ministan haka ta kasa cimma ruwa, to amma tuni wasu kungiyoyin fafatukar kare tarbiya ke cewa abin na tare da rashin tarbiya.