1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Jirgin ruwa ya kife da mutane

Ahmed Salisu
July 11, 2019

Rahotanni daga Nijar na cewar mutane 11 sun rasu bayan da wani jirgin ruwa ya kife da su a Tsibirin Gobir da ke da tazarar kilomita bakwai da birnin Maradi.

https://p.dw.com/p/3Lwpg
Nigeria Bodo-Fluss Ölverseuchung 10 Jahre später
Hoto: AFP/Y. Chiba

Hadarin dai ya faru ne lokacin da ake kokarin hayewa da fasinjojin da ke cikin jirgin. Tuni dai bayanai suka fara fitowa fili game da dalilin kifewar jirgin ruwan inda hukumomi suka ce yi wa jirgin lodin da ya wuce kima ne ya sanya kifewarsa.

Wannan ne ma ya sanya hukumomi a kasar ta bakin gwamnan jihar ta Maradi Zakari Umaru yin kira ga al'ummar yankin kan su guji yin dukannin wani abu da ka iya jawo faruwar irin wannan lamari nan gaba.