1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Karkare ba da sakamakon zabe

Mahaman Kanta/AHFebruary 25, 2016

Hukumar zabe mai zaman kanta a Janhuriyar Nijar CENI, ta sanar da kammala kidayan kashi 80 daga cikin 100 na yawan kuri'u da aka kada a zaben gama gari.

https://p.dw.com/p/1I2Y5
Niger Wahlzentrale Niamey
Cibiyar musamman ta tattara sakamakon zaben Nijar watauHoto: DW/A. Adamou

A cewar shugaban hukumar dai suna kyautata zaton kammala kidayan kuri'un yau, kasancewar sakamo na ci gaba da zuwa. Mai shari Ibrahim Boube, ya ce abun da ya rage bai taka kara ya karya ba.Ya danganta jinkirin da tantance dukkan kuri'u bayana an kawo cibiyar kidaya. Hakan a cewarsa ya zama wajibi don gudun yin kuskure a kidaya da ma sakamakon shi kansa.

Tun a ranar Litinin ne dai hukumar ta CENI ta sanar da gabatar da sakamako na karshe cikin kwanaki hudu.A daya hannun kuma jam'iyun kawance sun nuna bacin ransu bisa ga yadda aka tsara da ma gudanar da zaben a wadansu yankunan jihar Tahoua.Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin jam'iyar PNDS Tarayya da take shirya zabubuka kasancewar tana milki a yanzu.

To sai dai kuma, kusan a iya cewa wannan shi ne karo na farko da ake cin karo da jerin kura-kurai inda ake ci-gaba da samun korafe-korafe a game da tsarin zaben da wasu ke dora alhakin rashin kyawunshi ga hukumar zabe ta kasa, yayin da wasu kuwa, ke zargin magudi.