1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kokarin kawar da matsalar bakin haure

Abdoulaye Mamane Amadou AS
October 19, 2018

Tawagar ‘yan majalisar dokokin kasashen ECOWAS ko CEDEAO ta kammala wata ziyarar aiki a kasar tare da tattaunawa da hukumomi dangane da batun 'yan gudun hijira da bakin haure da ma hanyoyin bi wajen dakile matsalar.

https://p.dw.com/p/36qMd
Brasilien Migranten aus Westafrika in Maranhao
Hoto: picture-alliance/AP Photo/C. Pereira

Tsawon kwanaki ne dai majalisar dokokin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta shafe ta na zagaye a ciki da sakon jamhuriyar Nijar a wani yunkuri na kawo dauki da daukar matakin kawo karshen matsalar ta kwararar bakin haure da 'yan gundun hijira da ke bi ta barauniyar hanya daga kasashensu na Afirka don tsallakawa zuwa kasashen Turai.

Migration aus Afrika in der Nähe der Stadt Gohneima, Lybien
Shigar bakin haure nahiyar Turai ta teku na cigaba tada hankalin hukumomi a Turai da AfirkaHoto: picture-alliance/dpa/AP/Küstenwache Lybien

Tawagar mai jagorancin shugaban majalisar Moustapha Cisse Lo bayan ta yada zango a sassan kasar ciki har da Agadez don ganewa idonta daga bisani ta gana da hukumomin kolin kasar don tantance hanyoyin da majalisar zata bi wajen bayar da tata gudumawa kan matsalar da har yanzu ke neman ta gagari kundila, inda ya ce ''muddin ana son kawo gyara a cikin wannan matsalar da ke addabarmu dole mu yi gyara kan dokokinmu na shige da fice''.

Jamhuriyar Nijar dai na kan gaba wajen karba da wucewar bakin haure da 'yan gudun hijira da ke fitowa daga kasashen 15 mambobin na CEDEAO baya ga wasu tarin 'yan kasashen tsakiya da gabascin Afirka da ke bi ta kasar sannan duk da matakan da hukumomin ke cewar suna dauka wankin hula na neman ya kai ga kasashen dare, wannan ne ma ya sanya Kungiar Tarayyar Turai ta EU ware fiye da euro miliyan dubu daga nan zuwa shekaru 2020 wajen daukar matakin dakile kwarara ta bakin haure.