1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kotu ta dage shari'ar safarar jarirai da wata daya

Salissou Boukari
February 13, 2017

Wata kotu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar bisa tambayar lauyoyi, ta dage shari'ar da ta kamata a yi a wannan Litinin din kan batun safarar jarirai na kasa da kasa har ya zuwa ran 13 ga wata mai zuwa na Maris.

https://p.dw.com/p/2XTRG
Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Babbar kutun birnin Yamai na Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

Batun da ya shafi madugun 'yan adawar kasar Hama Amadou, da kuma wasu mutanen akalla 20 cikinsu har da tsohon minista kuma shugaban jam'iyyar CDS Rahama Abdou Labo, da wasu ma'aikatan bnki, da 'yan kasuwa, har ma da wani babban jami'in soja na kasar da kuma matayensu. Daya daga cikin lawyoyin da ke kare wadanda ake zargin ya ce dalilansu na neman dage shari'ar dai su ne na ganin sun samu sanin dukannin bayanai  a rubuce da lauyan da ke kare gwamnati ya ke da su kan wannan batu, ta yadda za su samu damar shirya mayar da nasu matarni.

Wannan batu dai na safarar jarirai, ya gurbata fagen siyasar Jamhuriyar ta Nijar tun yau da shekaru biyu, wanda hakan ya bai wa Shugaban kasar Issoufou Mahamadou damar yin yakin neman zabe shi kadai a shekarar da ta gabata ta 2016 yayin da Hama Amadou da shi ma ya yi takarar neman shugabancin kasar ke tsare a gidan kaso.