1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Nijar sun razana da rashin tsaro

May 16, 2019

Yawaitar hare haren da ke ritsawa da rayukan sojojin Janhuriyar Nijar na ci gaba da samun martanin talakawa da a yanzu ke cewar lamarin cikakken tsaro a kasar babu tabbas

https://p.dw.com/p/3IcHP
Militärmanöver Flintlock im Niger
Hoto: DW/A. M. Amadou

Al'umma na cigaba da bayyana tsoro yayin da hare haren ta'addanci ke ci gaba da aukawa Jamhuriyar Nijar, kasar da shugabanninta suka ayyana zaman makoki  karo na biyu a jere kasa da kwanaki goma, saboda 'yan kasar basu saba gani ba a tarihinta.


Batun karuwar munanan hare -haren ta'addancin na baya bayanan na kusan kwananki uku a jere na daga cikin abubuwan da ke ci gaba da kara daukan hankullan 'yan kasar matuka, wacce a shekarun baya al'ummar ta ke tsintar irin wadannan lamura a kafafen yada labarai na ketare.

Daga Tongo Tongo gari zuwa  lunguna da sako na kasar ta Nijar dai batun sukurkucewar tsaron ne suka mamaye wuraren zaman jama'a cikin mahawara mai cike da tambayoyin da ke bukatar amsa.


Daga cibiyoyin jam'iyyun siyasa zuwa wuraren firar jama'a  batun harin ta'addancin  da irin salon da 'yan ta'addar ke amfani da shi wajen kai harin na ci gaba da kara daukan hankali.


A yanzu dai hankulan 'yan kasar sun karkata ga batun tsaron yammacin kasar da ke kokarin kawar da gabashi ko da ya ke daga arewacin kasar ma kanwar ja ce.