1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Martani kan ziyarar shugaban Areva

Tila Amadou
February 20, 2017

Kungiyoyin fararen hula na jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da maida martani kan ziyara mukadashin kafanin Areva a wajen da ake tonon ma'adin Uranium a yankin Arlit a cikin dare.

https://p.dw.com/p/2Xver
Generatorgondeln von Areva
Hoto: picture-alliance/dpa

Ziyara ta mukaddashin kamfanin na Areva Philippe Varin a garin Arlit cikin dare ta jawo cece-kuce sosai musamman ma ga mazauna garin da kuma kungiyoyin fararen hula a jihar Agadez, inda yanzu haka su ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta. Guda daga cikin fitattun 'yan kungiyoyin fararen hula a Arlit Almoustapha Alhassan ya shaida wa wakiliyar DW a Agadez cewar wannan ziyara ta Mr. Varin na da ayar tambaya musamman ma da ya ke cikin dare ya yi ta. Talakawan na jihar Agadez ma dai ba a barsu a baya ba wajen tofa albarkacin bakunansu kan wannan ziyara, inda da dama ke cewar kamfanin ya shafe shekaru 40 ya na tonon Uranium a Agadez amma ya zuwa yanzu ba su gani a kasa ba.

Niger Uranabbau Uran
Wani ma'aikaci a mahakar Uranium da ke ArlitHoto: AREVA

Sanusi Mahaman da ke zaman guda daga cikin 'yan jihar cewa ya yi ya kyautu hukumomin jihar Agadez da ma shugabannin kananan hukumomi su fito don yi wa al'umma bayani kan wannan ziyara da mukaddashin shugaban na Areva ya kai yankin na Arlit, da nufin tantance makasudin zuwan nasa. Kungiyoyin fararen hula a jihar Agadez dai yanzu haka na ci gaba da Allah wadai da irin kawancen da Nijar ke da shi da kamfanin Areva, inda suka bayyana cewar ba a yin abin da ya dace wajen aikin  tonon karfen Uranium kana suna fatan nan gaba shugabannin su gyatta yadda tafiyar ke gudana kana a rika yi wa al'umma bayani game da yadda lamura ke wakana idan ana batu na tonon ma'adanin na Uranium, wanda ke jibge a karkashin kasa a jihar ta Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar.