1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Matashi ya dukufa a inganta hako rijiya.

Usman Shehu Usman
August 3, 2017

A Jamhuriyar Nijar wani matashi ne da ya karanci aikin ginin rijiya bayan yayen da ma'aikatar Offedes mai gina rijiyoyi a kasa a yanzu ya fada yankunan karkara don raba basira ga sauran matasa a filayen kiwo

https://p.dw.com/p/2hdkN
Brunnen in Zentral-Niger (Zinder)
Hoto: DW/Larwana Hami

Tuni dai makiyayan da ke cikin wahalhalun na rashin wadatar rijiyoyin, suka yi marhabin da shirin. Malam Jalla ya yi shekaru yana aikin hakar rijiya, dan asalin garin Belbeji wanda ke daya daga cikin ma’aikatan da tsofon kampanin Offedes ya yaye bayan da ya shahara wajen aikin gina rijiyoyi , a yanzu ya dauki fasahar koyar da matasa aikin gina rijiyoyi a filayen kiwo.

Da farko dai  ya bayyana irin zurfin gaba kasa na rijiyoyin da yake iya ginawa. To sai dai a cewar Jalla maginin rijiya a lokacin rikicin tawaye a wannan kasa ta Nijar, yayin da yake sabo-sabon fara aikin ya fuskanci kalubale mai yawa.

Mohamet Sidi shi ne  mai gari na Kandil Buzu, yankin da ya dace da rijiyoyin ban ruwa barkatai, karin haske yayi a kai, inda ya ce ya yi matukar frarin ciki bisa aikin Jalla Maigini.

Makiyayan dai a baya ya sun fiskanci matsala ta karamcin rijiyoyi da kuma lalacewar su, inda kan mai gyara yazo sai an ci kwakwa. To sai dai a yanzu wanan mataki na samun fasahar zamani zai taimaka matuka gaya.