1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin MSF kan korar jami'arta a Nijar

Mahaman Kanta LMJ
October 9, 2018

Kungiyar Likitoci na Gari na Kowa wato Médecin Sans Frontière/Doctors Without Borders ta mayar da martani kan korar jami'arta a Nijar.

https://p.dw.com/p/36FP5
Logo Medecins Sans Frontieres Ärzte ohne Grenzen MSF
Hoto: picture alliance /Ton Koene

Tun ranar da hukumomin Nijar din suka bai wa jami'ar Médecin Sans Frontière/Doctors Without Borders Dr Anne Pittet wa'adin sa'o'i 24 ta fita daga kasar, aka fara samun mabambantan ra'ayoyi dangane da wannan mataki. Cibiyar kungiyar da ke a Genève ta fiddo sanarwar goyon baya ga jam'iar, inda ta ce ta watsa wannan labarin ne da sunan kungiyar. Abin da ya janyo maharawa inda shugabannin kungiyoyin farar hula suka nuna takaicinsu ga kasawar gwamnati da kuma batun matsalar rashin magani a asibitoci. Ita dai Dr Anne Pittet ta bayyana cewa kanan yara 10 ke mutuwa ko wacce rana, a sansanin rikon yara masu fama da cutar tamowa a gundumar Magaria da ke yankin jahar Damagaram a Jamhuriyar ta Nijar sakamakon tsamarin da cutar ta tamowa da kuma zazzabin cizon souro suka yi.

Kimanin yara dubu 11.100 ne dai asibitin ya karba daga farkon watan Janairu zuwa 31 ga watan Agusta na wannan shekara, inda alkalumma suka nuna cewar yara dubu 3,311 aka karba a watan Agusta kadai. To sai dai batun rasuwar yara 10 a kullum ya tayar da hankalin likitoci da ma al'umma inda  Docta Atti Salifu mukaddashin daraktan asibitin ke cewar a tare suka gudanar da aikin da kungiyar ta MSF, sai dai wallafa rohoton basu da masaniya. To sai dai batun rasuwar yara 10 a kullum ya tayar da hankalin likitoci da ma al'umma inda  Docta Atti Salifu mukaddashin daraktan asibitin ke cewar a tare suka gudanar da aikin da kungiyar ta MSF, sai dai wallafa rohoton basu da masaniya. Kalamun wannan jami'a dai sun janyo mata fushi daga gwamantin kasar, inda nan take suka ba ta wa'adin sa'o'i 24 kan ta fice daga cikin kasar, bisa zarginta da wallafa rahoton kanzon kurege kan batun.