1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rikici kan zaben fidda gwani

Abdoulaye Mammane Amadou/ASDecember 8, 2015

Wasu 'yan jam'iyyar ANDP Zaman Lafiya a Nijar sun yi fatali da matakin uwar jam'iyyar na yin mubayi'a ga PNDS Tarayya a zaben shugabancin kasa maimakon a fidda dan takara.

https://p.dw.com/p/1HJTf
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: Seyllou/AFP/Getty Images

A karshen makon jiya ne dai kwamitin koli na zartarwar jam'iyyar ta ANDP Zaman lafiya ya bi sahun jerin wasu manyan jam'iyyun da ke mulki wajen nuna tasu mubayi'ar ga shugaban kasa Mahamadu Issoufou kuma dan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya da ke mulkin da zummar baiwa shugaban kasar damar lashe zabe tun daga zagaye na farko ta hanyar kin tsayar da dan takarar da zai iya kalubalantar shugaban a zaben da ke tafe.

Sai dai wannan matakin da kwamitin na koli ya dauka na ci gaba da haifar da cece-kuce tsakanin mabiya jam'iyyar ANDP din inda suke yi wa gabanninta kallon masu neman na shinkafa kawai da kuma kaifin tunanin dawwama a kan matsayinsu na mukaman siyasa. Malam Moussa Abdou mamba a kwamitin kolin jam'iyyar ta ANDP Zaman Lafiya ya ce kashi 90 bisa 100 na wanda suke goyon bayan wannan tsari sun amince da shi ne don cimma burinsu ba don tallafawa talaka ba.

Flash-Galerie Wähler in einem Wahllokal in Niger
Hoto: AP

Matakin da uwar jam'iyyar ta dauka na zuwa ne a yayin da hankalin wasu mambobin jam'iyyun kasar ya karkakata kan sabon salon matsayin da shugabanninsu ke dauka ta hanyar yin mubayi'a ga shugaban kasa tun ma ba a je zabe ba, abubuwan da masu fashin bakin siyasa ke yi wa kallon na iya taka wata mahimmiyar rawa wajan rugajewar jam'iyyun.

Hama Amadou bei der ersten Wahlrunde im Niger
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Tunni dai wannan lamarin ya kara cusa fargaba a zukatan wasu 'yan jam'iyyar ta ANDP din har ya saka su fara barin jam'iyyar kamar yadda kakakinta Moussa Abdou ya shaidawa wakilin DW a Yamai Abdoulaye Mammane Amadou. Mousa Abdou din ya ce ''jam'iyyar ANDP ta ji jiki sosai domin idan ka saurara za ka ji ana cewar 'yan jam'iyyar sun fita daga ciki.''

Ya zuwa yanzu dai kwamitin koli na jam'iyyar bai kai ga maida martani kan wannan batu ba amma tuni wasu kungiyoyin fararen hullar kasar suka fara tofa albarkacin bakinsu kan sabuwar badakalar da ta kunno kai a cikin jam'iyyu da kuma ta ke neman ta gagari kundila a gabanin zaben kasar, inda suke cigaba da yin Allah wadai da shi.