1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta bukaci tallafin kasashen duniya

March 1, 2014

Hukumomin a Jamhuriyar Nijar na neman tallafin kudade na cefa miliyan 195 a wannan shekara ta 2014, domin gudanar da wasu muhimman ayyuka na inganta rayuwa.

https://p.dw.com/p/1BHqM
Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012
Hoto: Getty Images

Wannan kira ya fito ne a wannan Juma'a (28.02.2014) a wani babban zaman taro da Firaministan kasar ta Nijar Brigi Rafini ya jagoranta, tare da wakillan kasashen duniya da na Majalisar Dinkin Duniya.

Da yake magana wurin wannan taro wakilin MDD a kasar ta Nijar Fodé Ndiaye, ya ce idan aka samu hada wadannan kudade, za'ayi amfani da su a fannoni da dama, da suka hada da batun 'yan gudun hijirar kasar Mali da ma na arewacin Najeriya dake cikin wannan kasa, tare da shirin ko ta kwana ga duk wata annobar cututuka da kan iya bayana.

Wakilin na MDD a kasar ta Nijar ya kara da cewa, cikin kudadan za'a sayi abinci, tare da inganta batun samar da ruwan sha masu tsabta, da batun kiwon lafiya da ma na ilimi a wannan kasa, inda fiye da kashi 80 cikin dari na al'ummar ke dogaro ne da Noman galgajiya.

Saidai wasu na ganin cewa duk da wadan nan matsaloli da wannan kasa ke fuskanta amma kuma tana fama da cece kucen siyasa na cikin gida.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar