1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta ce ta kashe 'Yan Boko Haram 260

Mouhamadou Awal BalarabeFebruary 12, 2015

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sha alwashin murkushe Boko Haram, inda kakakinsu ya ce tuni suka kashe 'ya'yan wannan kungiya da dama tare da kwace makamai a hannunsu.

https://p.dw.com/p/1Ea7u
Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Rundunar sojojin Jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa ta yi nasarar kashe 'yan Boko Haram 260 tun bayan da wasu kasashen Afirka suka hada karfi kwanaki shidan da suka gabata don sa kafar wando guda da mayakan. A lokacin da ya ke tsokaci a birnin Yamai kakakin rundunar sojojin Nijar Kanal Moustafa Michel Ledru ya kuma kara da cewa sun kame 'ya'yan na Boko Haram da dama tare da kwace wasu makamai, amma ba tare da yin karin haske ba.

Masu gaggwarmaya da makaman sun kadammar da hare-hare da dama a garuruwan Diffa da kuma Bosso da ke kudancin Nijar da kuma ke da iyaka da Tarayyar Najeriya. Kanal Ledru ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu saboda sojojin na Nijar sun dauki matakan kare rayuka da kuma dukiyoyinsu. Wannan dai ba ya rasa nasaba da kaurace wa matsugunansu da mazauna biranen biyu ke yi zuwa Damagaram sakamakon fargabar wasu karin hare-hare daga kungiyar Boko Haram.