1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta jajantawa kasar Chadi kan batun hari

Abdoulaye Mamane AmadouJune 16, 2015

Shugaban kasar Nijar da ke a matsayin shugaban hukumar raya Tafkin Chadi, ya aika sakon jajantawa ga takwaransa na Chadi Idriss Deby kan harin da aka kai a Ndjamena.

https://p.dw.com/p/1Fi6f
Mahamadou Issoufou
Mahamadou IssoufouHoto: DW/M. Kanta

Sanarwar da aka karanta ta gidan redio da talbijin din kasar ta Nijar, ta sanar da nuna rashin jin dadin gwamnatin kasar ga harin da aka kai a karon farko a birnin Ndjamena tun bayan da kasar ta Chadi ta tsunduma gadan-gadan cikin yaki kungiyar Boko Haram, sannan shugaban kasar ta Nijar Issoufou Mahamadou ya yi amfani da matsayinsa na shugaban hukumar raya Tafkin na Chadi ta CBLT, domin kira ga shugabannin manya-mayan kasashen duniya don tallafawa kungiyar a yakin da take da yan taadda na Boko Haram. Tuni dai masu sharhi ke tofa albarkacin bakinsu kan wannan sabon lamari da ya riski kasar ta Chadi, tare da yaba matakin da kasar ta Nijar ta dauka na bin sahun kasashen duniya wajan nuna alhininta ga abun da ya samu makwabciyarta kasar ta Chadi. Dr Sani Yahaya Janjuna wani mai sharhi ne a kan alamurran yau da kullun ya yi tsokaci inda ya ke cewa:

Masu sharhi sun yaba matakin da Nijar ta dauka.

" Irin yadda shugaban kasarmu Issoufou Mahamadou ya bada wannan sanarwa, na nuni da cewar har yau huldarmu na nan, kuma yarjejeniyar da munka yi na nan. Kuma bisa abubuwan da munka sanya hannu na yaki da 'yan taadda na nan har gobe. Mu na kawo goyon baya 100 bisa 100 a garesu kuma har gobe muna nan sai munga bayan wannan alamari, domin ba mamaki ko gobe su yi wa wata kasa irin abun da suka yi a Chadi, amma wannan ba zai sa kasashenmu su ja da baya ba."

Nigeria Tschadsee Konferenz
Hoto: State House, Abuja

Sai dai harin na kasar ta Chadi da ya yi sanadiyar hallaka mutane fiye da ashirin, na zuwa ne 'yan kwanaki kalilan da kammala wani taron koli na shugabannin raya Tafkin Chadi da suka yi a Abuja domin neman hanyoyin walwale matsalolin da ke addabar kasashen, taron da ya sanar da girka wata bataliayar soja mai kumshe da dakaru 8.700 domin yakar mayakan na Boko Haram. Sai dai a cewar Docta Yusuf Yahaya wani kwararre a fannin tsaro, kamata ya yi shuwagabannin kasashen na Tafkin Chadi su sauya wani sabon salon yaki.

Nigeria Tschadsee Konferenz
Hoto: State House, Abuja

Ya kamata hukumar CBLT ta canza salo.

" Su sauya salo su rage babatun da yawan magana kuma su bada kayan aiki ga sojojinsu, sannan su fadi abinda ya kamata sojojin su yi tunda ba diyansu ke yakin ba, ba kuma sojojin da ke karesu ke yakin ba ko kuma magoya bayansu na siyasa. Don haka sojojin da suke yaki su suka san abin da suke so, a basu hakinsu su, sannan a basu kayan da ya kamata na zamani kuma a yi shiru don shi yaki da taaddanci bai son yawan magana."

A halin yanzu dai hankali ya karkata kan irin martanin da kasar ta Chadi za ta mayar ganin cewar shugabanta ya sha ikirarin cewar ya san maboyar jagoran kungiyar Abubakar Shekau. Sai dai kuma a hannu daya wasu masu sharhi sun kasa walwale ayar tambaya kan irin matsayi da Rundunar dakarun sojan kasar Faransa ta Barkhan ke da shi kasashen na yankin Sahel cikinsu kuwa hard a kasar ta Chadi.