1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta Karfafa huldar tsaro da Amirka

Abdoulaye Mamane Amadou
November 8, 2017

Jamhuriyar Nijar da kasar Amirka da Nijar sun kaddamar da wani taron tattauna batutuwan tsaro tare da yin bitar ayyukan tsaron da suke ke yi tare don kare lafiyar al'umma a yaki da suke yi da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/2nGyt
Nigeria Soldaten in Diffa
Sojojin Nijar masu sintiri na yaki da 'yan ta'addaHoto: Reuters/J. Penney

Tun a tsakiyar watan Octoba na 2015 ne gwamnatocin kasashen biyu na Amirka da Nijar suka shinfida wani tsarin mai suna JCAP ko SGI, da ya shafi inganta tsaro da samar da kayayakin aiki ga jami'an tsaro na kasa. Babban makasudin taron na birnin Yamai shi ne duba inda aka kwana dangane da wannan hulda da ma yin nazari game da abubuwan da ke addabar kasashen biyu musamman ma Nijar da suka jibanci ayyukan ta'addanci da kasar ta Amirka ke taka muhimmiyar rawa wajen yaki da masu tayar da kayar baya.

Bangarorin biyu na Amirka da Nijar sun samu gamsuwa dangance da halin da kasashen biyu ke tafiyar da ayyukan wanda a ciki suka tabbatar da samun muhimman nasarori.  Manjo Ledru Moustapha Michel shi ne mai magana da yawun kawancen na kwamitin tsaron na kasashen Nijar da Amirka ya ce: "A yau idan ka dubi kasar mu ta Nijar duk da yake a na samun wasu 'yan matsaloli na tsaro jefi-jefi, to amma kuma babu ko da wani karamin yanki da ya fada a hannun wasu 'yan ta'adda ba, kuma ba'a iya cewar kasar na cikin yaki saboda haka sai mu ce mun gode Allah domin wannan ita ce babbar nasara".

USA Ankunft der toten US-Soldaten aus dem Niger
Sojojin Amirka dauke da daya daga sojojinsu da aka kashe a NijaHoto: picture alliance/AP Photo/L. Hiser/U.S. Army

Wannan haduwa na zuwa ne makonni biyar bayan wani hari da 'yan ta'adda suka kai wa ayarin sojojin Nijar da na Amirka a yankin Tillaberi mai makwabtaka da Mali wanda ciki sojojin da suka mutu har da na kasar ta Amirka guda hudu. Ko baya ga batutuwan tsaro tsarin na JCAP ko SGI na taimako a fannin bunkasa ayyukan sadarwa tare da daidaita hulda tsakanin soja da fararen hulla ta hanyar amfani da fasahohin wayar da kai, duk da yake sojan Amirka na da dama a kasar ta Nijar tun a shekarun 2000 a shekarar 2015 gwamnatin Mahamadou Issoufou ta sake sabunta huldar yarjejeniyar lamarin da yakai ga jibge sojojin kasar da dama da alkalumma suka ce sun haura 800 a kasar ta Nijar.