1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cafke wadanda suka tayar da hankali

Larwana Malam HamiJanuary 23, 2015

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tana ci gaba da cafke wadanda ake zargi da zanga-zangar da ta zama tashin hankali

https://p.dw.com/p/1EPn3
Niger Anti Charlie Hebdo Protest Polizeieinsatz 18.01.2015
Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

A birnin Damagaram na Jamhuriyar Nijar matakan cafke 'yan siyasa da 'yan farar hula gami da dalibai a wani mataki na tantance masu hannu a zanga-zangar da Musulmai suka gudanar, masana zamantakewar yau da kullum tare da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na ci gaba da mayar da martan.

Farkon samamen jami'an tsaron na cafke jama'ar da ake zargi da hannu a aika-aikar da ta biyo bayan zanga-zangar ta ranar Juma'ar da ta gabata dai kawo yanzu mutane 22 ke hanun hukuma da suka hada da 'yan siyasa malaman adinin Musulinci, da dalibai da kuma 'yan fararen hula.

Niger Anti Charlie Hebdo Protest Islam Koran 17.01.2015
Hoto: Reuters/T.Djibo

To sai dai a dangane da wannan kame-kame da hukumomin ke ci gaba da yi, shugaban Jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki Bazum Mohamed ya ce 'yan siyasa ne suke da alhakin duk abin da ya faru. A cewar Malam Haru almajirin Malam Saley daya daga cikin malaman addinin da aka capke malaminsu ba mai wa'azin tada fitina ba ne.

Jam'iyyu irin su MNSD Nasara da CDS Rahama kamen ya ritsa da magoya bayan su, haka batun ke gaban kotu. To amma a cewar Abduljalil dan majalisa da'ira daga tutar jam'iyyar CDS Rahama wasa wuka bai kada gaban doki. Tuni 'yan kungiyoyin fararen hula da ke bin irin abubuwan da ke tafiya ta bakin Abdulmajid Usseini na MPPAD suka koka da cewar kame wajibi ne amman akwai take doka.

Niger Anti Charlie Hebdo Protest Islam 17.01.2015
Hoto: Reuters/T.Djibo

Gwamnan Jihar Damagaram Kalla Muntari duk da bai yarda a nadi muryarsa ba ya tabbatar da cewar suna tattaunawa da malaman addinai da kuma sarakunan gargajiya domin ganin an kwantar da wutar rikicin.